Rundunar soji ta karyata rahotannin cewa Boko Haram sun kwace garuruwan Borno 6

Rundunar soji ta karyata rahotannin cewa Boko Haram sun kwace garuruwan Borno 6

- Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahotannin cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwa shida a jihar Borno

- Kakakin rundunar Birgediya Janar Sani Usman, ya karyata rahoton a wani sako da ya saki

- Ya ce lallai rahoton kwace garuruwan guda shida da aka ce yan ta’addan sun yi bata ne

Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahotannin cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwa shida a jihar Borno.

Daraktan labarai na rundunar, Birgediya Janar Sani Usman, ya karyata rahoton a wani sako da ya aikewa Channels TV a ranar Litinin.

Rundunar soji ta karyata rahotannin cewa Boko Haram sun kwace garuruwan Borno

Rundunar soji ta karyata rahotannin cewa Boko Haram sun kwace garuruwan Borno
Source: UGC

Ya ce lallai rahoton kwace garuruwan guda shida da aka ce yan ta’addan sun yi bata ne.

Sakon Birgediya Janar Usman na zuwa ne kwanaki kada bayan an kawo cewa ayyukan Boko Haram na karuwa a Baga da kuma rahoton cewa yan ta’addan sun kwace garuruwa shida a karamar hukumar Kukawa da ke Borno.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar soji ta kau da yan kunar bakin wake mata su 3

A baya mun ji cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwan Baga, Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da kuma Kukawa a jihar Borno.

Daily Trust ta ruwaito cewa wata babbar majiya ta sojoji da siyasa ne suka bayyana hakan a Maiduguri a ranar Lahadi, 30 ga watan Disamba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel