Muhimman maganganu 7 da Buhari yayi yayin kaddamar da kamfe din sa a Uyo

Muhimman maganganu 7 da Buhari yayi yayin kaddamar da kamfe din sa a Uyo

A yau ne dai, Juma'a 28 ga watan Disemba Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da gangamin yakin neman zabensa karo na biyu a garin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom dake a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya.

Taron gangamin yakin neman zaben dai ya samu halartar jiga-jigan jam'iyyar daga dukkan sassan kasar kama daga gwamnoni zuwa Sanatoci da 'yan majalisa, da ministoci da ma manyan masu fada aji na jam'iyyar a dukkan matakai.

Muhimman maganganu 5 da Buhari yayi yayin kaddamar da kamfe din sa a Uyo
Muhimman maganganu 5 da Buhari yayi yayin kaddamar da kamfe din sa a Uyo
Asali: Facebook

KU KARANTA: Mutum 2 ne kawai basu cin hanci da rashawa a Najeriya - Balarabe Musa

Legit.ng Hausa ta samu cewa shugaban kasar yayi jawabi gajere a wajen taron bayan dukkan kowa yayi nasa kuma ga kadan daga cikin muhumman batutuwan da ya tabo:

1. Buhari ya yi bayani kan tsaro inda ya tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram bata rike da gari ko daya a halin yanzu a Najeriya, don haka gwamnatinsa ta yi nasara a kan kungiyar.

2. Shugaban ya bayyana cewa a lokacin da ya karbi mulki a 2015, Boko Haram na rike da kananan hukomi kusan 17 a jihohin Barno da Yobe, amma a halin yanzu ba ta da iko da ko daya.

3. Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da tabbatar da tsaro da habbaka tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

4. Shugaban ya bayyana cewa an kwato kadarori da kuma kudade a yaki da ake yi da cin hanci da rashawa.

5. A bangaren tattalin arziki, ya bayyana cewa an samu ci gaba wajen samar da abinci a Najeriya ta hanyar inganta noma da kuma hana fasa kwaurin shinkafa.

6. Ya bayyana rashin aikin yi a matsayin matsala a kasar ganin cewa kashi 60 cikin 100 na 'yan kasar matasa ne.

7. Shugaban ya ce yanzu kasar ta samu zarafin ciyar da kanta abinci sabanin da da 'yan kasar ke shigowa da mafiya yawan abincin da suke ci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel