Wani da ya yiwa kanwarsa mai shekaru 15 ciki a Kano ya dora laifi kan shaidan

Wani da ya yiwa kanwarsa mai shekaru 15 ciki a Kano ya dora laifi kan shaidan

Mutanen unguwar Gagarawa da ke karamar hukumar Madobi na jihar Kano sunyi mamakin jin labarin wani Badamasi Abdullahi mazaunin unguwar da ya yiwa kanwarsa mai shekaru 15, Bara'atu Abdullahi.

Daily Nigerian ta gano cewa lamarin ya faru ne bayan mahaifin yarinyar, Abdullahi Haruna ya kore ta a gidansa saboda wani laifi da ta yi.

Hakan ya sa yarinyar ta koma gidan yayan ta da zama wadda ba shi da nisa daga gidan iyayensu.

Bayan ta koma gidan shi kuma yayan ta ya lalaba zuwa dakin Bara'atu inda suka sadu kuma hakan ya yi sanadiyar shigar ciki.

DUBA WANNAN: Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku

Wani da ya yiwa 'yar uwar sa mai shekaru 15 ciki a Kano ya dora laifi kan shaidan
Wani da ya yiwa 'yar uwar sa mai shekaru 15 ciki a Kano ya dora laifi kan shaidan
Asali: Twitter

A yayin da ta ke zantawa da manema labarai a Kano ranar Labara, Bara'atu ta amsa cewa ta sadu da yayan ta.

"Badamasi ne ya yi min ciki. Na koma gidan yaya na da zama ne bayan mahaifinmu ya kore ni daga gida saboda nayi masa laifi.

"Mahaifina ya ce in tafi gidan yaya na in zauna, gidan sa ba shi da nisa daga gidan mu. Kwana na biyu a gidan yaya na.

"A ranar da abin ya faru, yaya na Badamasi ya shigo dakina kuma muka sadu," inji ta.

Shima Badamasi ya amsa cewa shine ya yiwa kanwarsa ciki.

Ya ce shedan ne ya rinjaye shi ya aikata wannan danyen aikin kuma ya roki afuwa daga hukuma.

"Eh, ni ne nayi mata ciki. Shedan ya rude shi na aikata hakan. Ba haka hali na ya ke ba, bana kaunar tuna abinda ya faru. A rikice na ke. Amma nayi nadamar abinda nayi. Ina neman afuwa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel