Kiwon lafiya: Shisha na dauke da sinadarin da ke haddasa cutar kansa - Rahoton UAE

Kiwon lafiya: Shisha na dauke da sinadarin da ke haddasa cutar kansa - Rahoton UAE

- Wani bincike da ya fito daga UAE, ya bayyana cewa akwai sinadarin karafa da ke haddasa cutar kansa a jikin dan Adam a cikin kayayyakin da ake hada Shisha

- Masana kimiyya a Sharjah da Abu Dhabi sun gano cewa medwakh da shisha na dauke da karafan nickel, chromium, copper da kuma zinc

- Bincike ya biyo wani nazari da aka gabatar a farkon wannan shekarar, wanda ya bayyana yawan sinadarin nicotine da tar a cikin medwakh, fiye da yadda yake a cikin sigari

Wani bincike da ya fito daga hadaddiyar kungiyar daular Laraba UAE, ya bayyana cewa akwai sinadarin karafa da ke haddasa cutar kansa a jikin dan Adam a cikin medwakh da kuma kayayyakin da ake hada Shisha da su, da kuma sigari.

Masana kimiyya a Sharjah da Abu Dhabi sun gano cewa idan aka hadata da sigari, gaba daya sinadarin medwakh da shisha na dauke da karafan nickel, chromium, copper da kuma zinc, masu yawan gaske.

Bincike ya biyo wani nazari da aka gabatar a farkon wannan shekarar, wanda ya bayyana yawan sinadarin nicotine da tar a cikin medwakh, fiye da yadda yake a cikin sigari.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Dalilin da yasa Buhari zai samu goyon bayan jihar Akwa Ibom - APC

Kiwon lafiya: Shisha na dauke da sinadarin da ke haddasa cutar kansa - Rahoton UAE
Kiwon lafiya: Shisha na dauke da sinadarin da ke haddasa cutar kansa - Rahoton UAE
Asali: UGC

Masana kimiyya suka ce wannan na nuni da cewa masu shan sigari na iya kamuwa da babbar matsaar rashin lafiya da ta hada da cutar kansar huhu da kuma cutar 'coronary artery'.

"Medwakh da bututun shisha na dauke na gargajiya basa dauke da abun tacewa, don haka karafa masu hatsari zasu shiga cikin huhu kai tsaye, wanda zai haifar da cututtuka da suka da na huhu da kuma na baki, kamar cutar 'cardiovascular," a cewar Ayesha Mohammed, wata lamar ilimin 'chemistry' a jami'ar Sharjah, kuma jagorar wannan rahoto.

"Ba zan taba cewa mutum ya sha dokha [medwakh] da shisa ba saboda basu da mataci, don haka karafa masu hatsari zasu shiga cikin mutum kai tsaye fiye da illar shan sigari, kuma zai haifar da cutar kansa.

"Shan medwakh kamar bindiga ce mai cike da harsasai, kuma lokaci ne zai dana kunamar harba ta."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel