An sake kai wani kazamin farmaki a wani kauyen jihar Zamfara

An sake kai wani kazamin farmaki a wani kauyen jihar Zamfara

Labarin da muke samu da dumin sa shine na wasu 'yan bindiga da suke kashe akalla mutum 15 a kauyen Magamin Diddi dake a cikin yankin karamar Hukumar Muradun ta jihar Zamfara dake Arewa maso yammacin Najeriya.

Bayanai daga majiyoyin mu da kuma wasu da lamarin ya auku a kan idon su sun ce 'yan bindigar sun auka kauyen ne bayan sallar azahar din ranar Asabar da ta gabata, inda kuma suka rika harbi kan mai uwa-da-wabi.

An sake kai wani kazamin farmaki a wani kauyen jihar Zamfara

An sake kai wani kazamin farmaki a wani kauyen jihar Zamfara
Source: UGC

KU KARANTA: An gano kudin takalmin da Buhari ke sawa

Legit.ng Hausa ta samu kuma cewa abin takaicin shine har ya zuwa yanzu jami'an tsaro ko hukumomin da abun ya shafa a jihar ba su ce komai ba game da wannan al'amari.

Sai dai wani mutumin yankin da lamarin ya auku a kan idon sa ya ce mutanen kauyen da dama ne suka jikkata sakamakon harbe-harben da barayin suka yi tsawon lokaci ba tare da samun dauki daga jami'an tsaro ba.

Jihar Zamfara tana fama da hare-haren 'yan fashin shanu da masu satar mutane don neman fansa, wadanda suka tagayyara yanki wanda a jiya ma har mun kawo maku yadda wani Shehi Malamin addinin musulunci daga Kano ya yi kira ga shugaba Buhari ya kara tura jami'an tsaro a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel