Hisbah ta kama sangartattun matasa 25 a Kano

Hisbah ta kama sangartattun matasa 25 a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce jami'anta sun kama matasa 25 da aka samu suna aikata laifuka daban-daban a birnin Kano.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa duk wani halin rashin da'a haramun ne a karkashin dokar shari'a ta jihar Kano.

Jami'in hulda da jama'a na Hisbah, Malam Adamu Yahaya ya shaidawa NAN a Kano a ranar Laraba cewa wadanda aka kama sun hada da mara 16 da maza 9.

Ya yi bayanin cewa an kama matasan ne a ranar Talata a Birigade Quaters da ke karamar hukumar Nasarawa yayin wani samame na musamman da jami'an hukumar suka kai.

Hisbah ta kama sangartattun matasa 25 a Kano

Hisbah ta kama sangartattun matasa 25 a Kano
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An gurfanar da wani matashi a kotu saboda saduwa da akuya

Ya ce an kai samamen ne bayan samun rahoto cewa wasu matasa na shaye-shaye da rawa da cudanya da mata a wani gidan haya a unguwar da dadare.

Ya ce cikin wadanda aka kama akwai mata da maza wanda shekarunsu ke tsakanin 30 zuwa 32.

Jami'an mu sun tafi gidan misalin karfe 11 na dare a ranar Talata inda suka kama mutane 25 a gidan," inji Yahaya.

Ya kara da cewa bayan an gudanar da bincike an gano 13 daga cikinsu mashaya muggan kwayoyi ne, haka yasa aka mika su ga makarantar gyara tarbiya da ke karamar hukumar kiru na jihar Kano domin su sauye halayensu su zama 'yan kasa nagari.

Yahaya ya ce sauran matasan da aka kama ba 'yan asalin Jihar Kano bane kuma ya yi kira ga iyayensu su rika kokarin bayar da tarbiya mai kyau ga yaransu.

Ya kuma shawarci matasa a jihar su guji aikata duk wani aikin masha'a, su kasance masu tsoron Allah a kowanne lokaci, su guji bin abokanen banza su kuma dage suyi rayuwa mai amfani a duk inda suka samu kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel