Wasu fitsararrun 'yan madigo sun takulo tsuliyar dodo a garin Kano

Wasu fitsararrun 'yan madigo sun takulo tsuliyar dodo a garin Kano

Wasu fitsararrun yan mata da ake zargin su da laifin aikata madigo za su fuskancin fushin hukuma a jihar Kano dake Arewa maso yammacin Najeriya idan har kotu ta tabbatar da laifin da ake zargin su da shi.

Gwamnatin ta jihar Kano dai da ke arewacin Najeriya ta ce za ta kai matan da take zargi da madigo kotun shari'ar musulunci bayan an kama su suna shirin bikin aure a tsakanin su.

Wasu fitsararrun 'yan madigo sun takulo tsuliyar dodo a garin Kano
Wasu fitsararrun 'yan madigo sun takulo tsuliyar dodo a garin Kano
Asali: Twitter

KU KARANTA: An sace wata tsaleliyar budurwa kwana daya kafin auren ta

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa, Mataimakin kwamandan Hisbah na jihar Isa Sani ya shaida wa majiyar mu cewa sauran wadanda za a kai kotun sun hada da mutane 10 wadanda suka halarci wurin da aka shirya bikin, da kuma wanda ya bayar da hayar gidan da aka shirya bikin.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a ranar Litini ce hukumar ta damke matan a unguwar Sabon Garin Kano, kuma har yanzu hukmar na rike da guda biyu daga cikin su.

Mai magana da yawun kotun shari'a ta Kano, Baba Jibo Ibrahim ya ce suna sane da mmaganar sannan su na jiran hukumar Hisbah ta kawo maganar gaban kotun domin a fara sauraron karar.

Dokar Najeriya dai ta haramta auren jinsi guda, kuma duk wanda aka kama da laifin zai iya kwashe kimanin shekara 14 a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel