Zama babu aure ya zama nakasa - Hukumar lafiya ta duniya

Zama babu aure ya zama nakasa - Hukumar lafiya ta duniya

- Jami’an hukumar lafiya ta duniya sun sanar da cewa zama babu aure nakasa ce

- Tace maza da mata da ke burin mallakar iyalai da magada amma basu samu abokan aure ba toh nakasassu ne

- Wannan sabon sanarwar ya haifar da mamaki da ban al’ajabi ga miliyoyin mutanen da ke fama da kadaici a fadin duniya

Jami’an hukumar lafiya ta duniya sun sanar da cewa zama babu aure nakasa ce.

Wannan sanarwa ta WHO ya bayyana cewa maza da mata da ke burin mallakar iyalai da magada amma basu samu abokan aure ba toh nakasassu ne.

Zama babu aure ya zama nakasa - Hukumar lafiya ta duniya

Zama babu aure ya zama nakasa - Hukumar lafiya ta duniya
Source: Instagram

Wannan sabon sanarwar ya haifar da mamaki da ban al’ajabi ga miliyoyin mutanen da ke fama da kadaici a fadin duniya.

WHO ta jajirce akan matsayarta cewa duk mutumin da ke zaune a doron kasa yana da ikon hayayyafa. Amma sai gashi wasu mutane imma su fada harkar soyayya da jinsu su sai kuma wasu so gaza samun abokan zaman da suke buri.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta shirya gabatar da mafi karancin albashi ga majalisar dokoki - Buhari

Sannan sabon bayanin WHO ya nuna cewa rashin samun cikar burin mutum daidai yake da rashin haihuwa.

Wannan ya janyo hankula mutane da dama. Wasu na ganin kamata yayi WHO ta mayar da hankali kan likitanci maimakon ra’ayin kanta na daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel