Abun bakin ciki: Yaro dan shekara 9 ya fada rijiya a Kano

Abun bakin ciki: Yaro dan shekara 9 ya fada rijiya a Kano

- Wani karamin yaro Haliru Abdullahi, mai shekaru tara ya fada rijiya a jihar Kano yayinda yake wasa day an uwansa yara a kusa da wata rijiya

- Lamarin ya faru ne a kauyen Kofar Kudu da ke karamar hukumar Gaya da karfe tara na safiyar Lahadi

- Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Mohammed ya bayyana hakan

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Mohammed ya bayyana cewa wani karamin yaro Haliru Abdullahi, mai shekaru tara ya fada rijiya.

Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba a lokacin da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kano.

Ya ce wannan abun kaicon ya faru ne a kauyen Kofar Kudu da ke karamar hukumar Gaya da karfe tara na safiyar Lahadi.

Abun bakin ciki: Yaro dan shekara 9 ya fada rijiya a Kano

Abun bakin ciki: Yaro dan shekara 9 ya fada rijiya a Kano
Source: Twitter

‘‘Mai Unguwar kauyen Hamza Abullahi a ranar Lahadi da safe ya sanar da mu cewa Haliru ya fada wannan rijiya ne a dalilin wasan da ya je yi da abokanan sa a kusa da rijiyar.

‘‘Daga nan kuwa muka kokarin ceto wannan yaro amma hakan bai yiwu ba. Kafin a ciro shi ya riga mu gidan gaskiya."

KU KARANTA KUMA: Kaso 90 na yan Najeriya sun yanke shawarar zabar Atiku - Fayose

A karshe Mohammed ya yi kira ga iyaye da su rika kula da walwalan ‘ya’yan su domin guje wa irin haka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel