Maganar wai ni na jawo gazawar gwamnatin Buhari zancen banza ne - Martanin Jonathan

Maganar wai ni na jawo gazawar gwamnatin Buhari zancen banza ne - Martanin Jonathan

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce sam ba ayi masa adalci ba, da aka alakanta shi da zama silar gazawar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari

- A baya dai Garba Shehu ya zargi Jonathan da umurcitar mukarrabasa na kin bada hadin kai ga kwamitin musayar mulki wanda ya kawo tsaikon nadin ministoci

- Sai dai Jonathan ya ce akwai bukatar Shehu ya je ya nemi ilimi na sanin yadda ta kasance a lokacin da zai mika mulki ga Buhari

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce sam ba ayi masa adalci ba, da aka alakanta shi da zama silar gazawar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta hanyar sanya dar dar a zukatan masu saka hannun jari a cikin watanni 6 na shugabancinsa.

Ya bayyana hakan ne a okacin da yake mayar da martanai kan wani jawabi da Garba Shehu, mai magana da yawun fadar shugaban kasa, ya yi, a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels TV a ranar Litinin.

A baya dai Shehu ya zargi Jonathan wanda a cewarsa ya umurci mambobin mukarraban gwamnatinsa da su ki bada hadin kai ga kwamitin musayar mulki, yana mai cewa wannan ne dalilin da ya sanya gwamnatin Buhari ta kasa aikata katabus.

KARANTA WANNAN: 2018: Mun saka jarin $100m a Nigeria - Gwamnatin kasar Sin

Maganar wai ni na jawo gazawar gwamnatin Buhari zancen banza ne - Martanin Jonathan

Maganar wai ni na jawo gazawar gwamnatin Buhari zancen banza ne - Martanin Jonathan
Source: Twitter

Sai dai da yake mayar da martani cikin wata sanarwa a madadinsa, daga Ikechukwu Eze, mai magana da yawunsa, Jonathan ya yi mamakin yadda gwamnati mai neman tazarce zata buge da neman mafakar da zata dora gazawarta akansu.

Jonathan ya ce akwai bukatar Shehu ya je ya nemi ilimi na sanin yadda ta kasance a lokacin da zai mika mulki ga Buhari, kuma sam bashi da alaka da rashin nada ministoci da Buhari ya gaza yi aka lokaci.

Ya ce aikin kowacce gwamnati ce ta nemi hanyoyin da zata bunkasa al'umma da kuma gyara siyasarta, yana mai karawa da cewa: "Duk gwamnatin da ta gaza yin haka, ta gaza nuna kwarewarta wajen shugabanci, to kuwa ta yi kuka da kanta akan gazawarta, ba wai ta rinka gogawa wasu mutane kashi ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel