Zargin cin hanci: Duba tambayoyi 10 da Atiku ya yiwa Buhari

Zargin cin hanci: Duba tambayoyi 10 da Atiku ya yiwa Buhari

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya amsa masa wasu tambayiyi 10 kan cin hanci da rashawa, wanda a cewarsa gwamnatin shugaban kasar kanta na cikin cin hanci da rashawa tsundum, ba kamar yadda take ikirarin yakar rashawar ba.

A cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara ta fuskar watsa labarai, Paul Ibe, da aka rabawa manema labarai a Abuja, Atiku ya kalubalanci shugaban kasar ne, biyo bayan ziyarar da tsohon skaataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawan ya shiga fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 13 ga watan Dismba, 2018, inda aka tarbe shi da sha tara ta arziki.

An kori Lawal daga ofishinsa ne sakamakon zargin cin hanci da rashawa.

KARANTA WANNAN: Jihar Legas: PDP zata samu nasara kan APC da tazarar kuri'u masu yawa - Agbaje

Zargin cin hanci: Duba tambayoyi 10 da Atiku ya yiwa Buhari
Zargin cin hanci: Duba tambayoyi 10 da Atiku ya yiwa Buhari
Asali: Facebook

Tambayoyin da Atiku Abubakar ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amsa masa sune:

"Wanene ya sake dawo da Maina tare da kara masa matsayi har sau biyu a lokaci daya?

"Wanane ya mallaki babban gidan Ikoyi da kudinsa ya kai $42m?

"Me aka yiwa mai tsaron Aisha Buhari wanda ya yi babakere da N2.5bn?

"Me ya sa ba yi bincike kan kwantiragin da kamfanin NNPC ya bayar na $25bn ba tare da ka'ida ba?

"Me ya sa har yanzu ba a kori wadanda suke da hannu a kutsen Buhari na kasafin kudi ba ko kuma aka gurfanar da su gaban kotu?

"Yaushe ne za a gurfanar da Babachir gaban kotu?

"Me yasa kudin tallafin mai ya linka duk da cewar farashin man ya linka shima?

"Me yasa shugaban kasa Buhari ya janye dakatarwar da aka yiwa shugaban hukumar NHIS, Usman Yusuf, kafin matsin lambar jama'a ya tursasashi dakatar da shi? Me ya sa har yanzu ba a kaishi kotu ba?

"A watan Mayu, kungiyar bin diddigi don tabbatar da adalci ta kasa da kasa tayi gargadi cewar Buhari ya kara kudaden da ake warewa tsaro da kashi 600%, sai dai har yanzu sojoji basu da makamai kuma 'yan ta'adda na ci gaba da kashe su. Shin ina kudaden suke shiga ne?

"A watan Fabreru, Buhari ya cire $1bn daga asusun rarar danyen mai don yaki da ta'addanci, sai dai shugaban hafsan sojin kasa, ya ce sojoji basu da makamai, jim kadan bayan harin Metele."

Sanarwar ta ce wadannan tambayoyi dama wasunsu, suna bukatar amsa daga shugaban kasa Buhari cikin gaggawa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel