Jiya ba yau ba: An gano kabarin wani malamin da yayi zamani da Fir'auna

Jiya ba yau ba: An gano kabarin wani malamin da yayi zamani da Fir'auna

Mahukunta a kasar Masar sun sanar da gano wani hubbare da ake kyautata zaton na wani babban jagoran addinin mutanen da wanda ya kai kusan shekaru dubu hudu da dari biyar da mutuwa.

Mun samu cewa dai an dai gano hubbaren ne a daya daga cikin katafaren yankin Saqqara mai dadden tarihi da ake da dalar Masar irin ta zamanin da.

Jiya ba yau ba: An gano kabarin wani malamin da yayi zamani da Fir'auna
Jiya ba yau ba: An gano kabarin wani malamin da yayi zamani da Fir'auna
Asali: Getty Images

KU KARANTA: DSS sun gurfanar da wani jigo na 'yan Biafra a kotu

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa tuni ma'aikatar adana kayayyakin tarihi ta masar ta ce hubbaren na wani babban malamin addini ne na gidan sarauta da iyalansa a lokacin daula ta biyar ta mulkin fir'aunan.

Bangon hubbaren na dauke da zane mutum-mutumin mutanen gidan da kuma wasu zane-zane na kawa da ke nuna irin wasu ayyukan da sukeyi kamar tuka jirgin ruwa, farautar tsunbtsaye da hadaya.

Sakatare janar na majalisar koli da ke kula da kayyakin tarihi na kasar ta Masar, Dokta Mostafa Al-Waziri, ya ce a hubbaren akwai wasu sako-sako wanda ke nuna cewa akwai alamomin wasu tarin kayayanki tarihi adane acikinsa.

A wannan lahadin dai ake shirin soma aikin tono hubbaren wanda ake saran a sake gano wasu abubuwa tarihi da dama a ciki.

Ga dai hotunan nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel