Hukumar FIRS ta tara ma gwamnatin Buhari makudan kudi N5,000,000,000,000

Hukumar FIRS ta tara ma gwamnatin Buhari makudan kudi N5,000,000,000,000

Ta tabbata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tottoshe ramukan da kudaden gwamnati suke sulalewa, bayan sanarwar da hukumar tara harajin kudaden gwamnatin tarayya, FIRS ta fitar na cewa ta tara ma gwamnati makudan kudade da suka kai naira tiriliyan biyar (N5,000,000,000,000)

Legit.com ta ruwaito shugaban hukumar FIRS, Babatunde Fowler ne ya bayyana haka a yayin zantawa da manema labaru a ranar Laraba 12 ga watan Disamba, inda yace zuwa mako na biyu na watan Disamba sun tara naira Tiriliyan biyar.

KU KARANTA: Za ayi jana’izar dakarun Sojojin Najeriya 100 da mayakan Boko Haram suka halaka

Sai dai yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba har sai sun tara naira tiriliyan biyar da biliyan dari uku kafin shekarar 2018 ta kare, watau yana nufin suna fatan zasu kara akalla kudi naira biliyan dari uku akan kudaden da suka tara zuwa yanzu.

Hukumar FIRS ta tara ma gwamnatin Buhari makudan kudi N5,000,000,000,000
Babatunde Fowler, shugaban FIRS
Asali: Facebook

Idan har FIRS ta cika burinta na tara naira tiriliyan biyar da biliyan dari uku, ya zamto kenan hukumar ta kafa tarihin da ba’a taba kafawa ba a Najeriya, saboda a tarihinta, mafi yawan adadin kudinda ta taba tarawa a shekara shine naira tiriliyan biyar da biliyan bakwai a shekarar 2012.

Sai dai masana na ganin FIRS ta cancan yabo da jinjina ko a haka da ta tara naira tiriliyan biyar, a yanzu da farashin mai ya karye rugu rugu, inda farashin gangan mai yake hawa da sauka a tsakanin dala 50 da dala 70, amma a shekarar 2013 yana tsakanin dala 100 da dala 120.

A jawabinsa, shugaban FIRS, Babatunde Fowler ya bayyana farin cikinsa da wannan cigaba da suka samu a hukumar, inda yace hakan ba zai yiwu ba sai da gudunmuwar da suka samu daga fadar shugaban kasa, ma’aikatan kudi, hukumar JTB da sauran masu ruwa da tsaki.

“Muna fatan zamu kai naira tiriliyan 5.3 zuwa karshe shekara, wanda zai zamto haraji mafi yawa da FIRS ta taba tarawa a tarihinta, kuma ina fatan da wannan karin kudin, gwamnatin tarayya, ya jihohi da ta kananan hukumomi zasu kara kaimi wajen gudanar da ayyukan cigaba don amfanin jama’a.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel