Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta

Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta

Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta yi karin haske game da matsayin Ali Nuhu a wajenta musamman ma dai a harkokin masana'antar.

Jarumar wacce ta ce ta fito a fina-finai da dama da ta kiyasta da 'sama da 50', ta shaida wa majiyar mu ta BBC a lokacin da ta zanta da ita kai tsaye a dandalin sadarwar zamani na Facebook cewa fitattcen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya wuce matsayin aboki a wajenta.

Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta
Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta
Asali: Facebook

KU KARANTA: Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta fadi sirrin tsawon rai

Legit.ng ta tsinkayi jarumar na cewa "Ba zan kira Ali Nuhu aboki ba, ya wuce matsayin aboki."

"Yadda zan zauna na yi magana da sauran jarumai, ba zan iya yi da Ali Nuhu ba," in ji Nafisa.

Ta ce Ali Nuhu ne sanadin fara zuwanta Kannywwod.

Nafisa Abdullahi dake zaman daya daga cikin jaruman da ke da farin jini sosai a fina-finan Kannywood ta kuma bayyana yadda ta soma shiga harkar fim bayan ta hadu da jarumi Ali Nuhu a shekarun baya a jihar Bauchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel