KEDCO sun yankewa Mutanen Zariya wuta saboda rashin biyan kudin lantarki
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mafi yawan mutanen Zariya sun shiga cikin wani mugun duhu bayan Kamfanin raba wuta na KEDCO ta yanke wutan lantarki a wurare da-dama na cikin Birnin a makon jiya.

Asali: Depositphotos
Kamar yadda labari ya zo mana, Ma’aikatan KEDCO sun datse wutar ne a dalilin rashin biyan kudin lantarki a Yankin. Sai dai wannan mataki da KEDCO ta dauka yana da alaka da sha’anin tsaro da kuma lamarin siyasar Jihar Kaduna.
Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Mai Girma Injiniya Aliyu Idris Ibrahim yayi kokarin lallabar KEDCO har ofishin su, da su hakura da batun yankewa jama’a wuta, amma duk da haka Ma’aikatan kamfanin ba su fasa abin da su ka shirya ba.
Idris Ibrahim, ya nemi a hakura da yanke wutan Garin ne saboda la’akari da sha’anin tsaro. Wani Hadimin Shugaban karamar Hukumar yace bata-gari na iya aikata wani mugun aiki a daidai wannan lokaci da ake cikin matsanancin duhu.
KU KARANTA: Kwana sun kare: An yi jana’izar wani Sarki da ya rasu a Jihar Kaduna
Wannan dai bai hana Ma’aikatan yankewa jama’a wuta a gidajen na su ba. Hakan ya jawo surutu iri-iri da korafe-korafe. Wasu Mazauna Yankin sun bayyana cewa an yi wanann ne domin kawowa yakin neman zaben Shugaba Buhari cikas a 2019.
Kamfanin na KEDCO dai yayi wa Mutanen cikin Garin na Zariya kudin goro, inda aka yanke wuta a kusan ko ina. Kawo yanzu dai Ma’aikatan Kamfanin sun ki yi wa ‘Yan Jarida bayanin abin da ya sa su kayi wannan aiki a Yankin na Jihar Kaduna.
Manyan mutane da sauran masu fada a ji, su na cigaba da kokarin shawo kan Ma’aikatan kamfanin da ke raba wuta a Jihar Kaduna da ayi hakuri a dawowa Jama’a da wuta amma har yanzu abin ya ci tura.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng