Sabon rikici ya mamaye PDP: Yan takara 2 sun fara yakin zaben kujerar gwamna a Ogun
- Rikicin da ya mamaye jam'iyyar PDP a jihar Ogun ya kara tsamari a ranar Litinin, yayin da Buruji Kashamu da Ladi Adebutu, suka kaddamar da yakin zabe
- Shi dai Mr Kashamu, shine dan takarar gwamnan jihar da hukumar INEC ta bayyana sunansa, sai dai shuwagabannin PDP na kasa sun baiwa Mr. Adebutu tutar takarar
- A baya, jam'iyyar PDP ta dakatar da Mr Kashamu da shuwagabannin jam'iyyar na jihar karkashin Dayo Bayo. Sai dai sun samu nasara kan jam'iyyar a kotu
Rikicin da ya mamaye jam'iyyar PDP a jihar Ogun ya dauki wani sabon salo tare da kara tsamari a ranar Litinin, yayin da 'yan takarar kujerar gwamnan jihar guda biyu, Buruji Kashamu da kuma Ladi Adebutu, suka kaddamar da yakin zabensu a wurare daban daban, don fafatawa a zaben 2019.
Mr Kashamu, wanda hukumar INEC ke rike da sunansa a matsayin halastaccen dan takarar gwamnan jihar ya kaddamar da yakin zabensa a garin Ijebu-Igbo, yayin da Mr Adebutu, wanda uwar jam'iyyar PDP ta kasa ta bashi tutar takarar kujerar gwamnan jihar, ya kaddamar da nashi a Abeokuta.
Dubunnan masoyan 'yan takarar biyu sun cika filayen da yan takarar suka gudanar da wannan gangamin yakin zabe, a hannu daya kuwa, kowanne dan takara na ikirarin shine halastaccen dan takarar jam'iyyar a jihar.
KARANTA WANNAN: 2019: PDP ta yi watsi da Kashamu, ta mika tuta ga 'yan takarar gwamnonin jihohi 3

Source: Twitter
Magoya bayan Mr Kashamu na tutiya da cewa hukumar INEC ta san da zaman dan takarar nasu, sai dai magoya bayan Mr Adebutu na cewa baiwa dan takararsu tutar takarar gwamnan jihar daga uwar jam'iyyar ta kasa ya tabbatar da cewa shine halastacce.
Tsagin jam'iyyar PDP na jihar sun gudanar da zaben fitar da gwamni daban daban, sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana Mr Kashamu a matsayin halastaccen dan takarar jam'iyyar a jihar bayan wani hukunci da kotu ta yanke.
A baya baya dai jam'iyyar PDP ta dakatar da Mr Kashamu da shuwagabannin jam'iyyar na jihar karkashin Dayo Bayo. Sai dai sun samu nasara kan jam'iyyar a karar da suka shigar da ita kotu.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng