Na umarce shi ya kawo sassan jikin mutum ne domin ya tsorata - Wani boka

Na umarce shi ya kawo sassan jikin mutum ne domin ya tsorata - Wani boka

- An kama wani mutum dauke da kan dan adam da kuma hannu yayin da ya ke hanyarsa ta zuwa gidan boka

- Mutumin ya ce bokan ya umurci ya kawo sassan jikin domin ya yi masa asirin samun arziki saboda bayan samun kasuwa a sana'arsa

- Sai dai bokan da aka damke shi ya ce ya fadawa mutumin ya kawo sassan jikin dan adam ne domin ya dena damunsa

Wani boka, Amos Sulaiman ya ce ya umurci wani, Supo Bamidele da ya zo wajensa neman taimako cewa ya kawo kai da hannun dan adam ne wai saboda ya tsoratar dashi daga yunkurin yin asirin neman arziki.

Suleiman wanda kwamishinan 'yan sanda na jihar Osun, Mr Fimihan Adeoye ya gabatarwa manema labarai tare da wanda ya zo wajensa naiman taimakon ya ce bai taba yiwa wani asirin samun kudi ba.

Na umarce shi ya kawo sassan jikin mutum ne domin ya tsorata - Wani boka
Na umarce shi ya kawo sassan jikin mutum ne domin ya tsorata - Wani boka
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Ganduje ya wakilci Buhari a nadin sarautar da aka yi masa

Adeoye ya shaidawa manema labarai cewa an kama Bamidele ne dauke da kan dan adam da aka guntule tare da hannuwa a garin Ile Ife, bayan kama shi ya shaidawa 'yan sanda cewa bokansa ne ya umurci ya kawo sassan jikin na adam domin ayi masa asiri.

A yayin da ya ke bayanin abinda ya faru tsakaninsa da Bamidele, Suleiman ya ce, "Ni mai bayar da magani ne kuma ina aiki a Ile-Ife. Na gaji wannan sana'a daga mahaifina ne kuma bamu yiwa mutane asirin kudi.

"Bana muggan aiki ko asirin samun kudi. A watanni 4 da suka wuce, Bamidele ya taso ni a gaba domin in taimaka masa saboda kasuwancin sa baya tafiya yadda ya kamata.

"Ya hana ni sakat shi yasa na fada masa ya kawo kan dan adam da hannu. Niyya ta shine hakan zai sa ya dena damu na. Ban taba tsammanin zai tafi ya nemo sassan jikin dan adam din ba."

A bangarensa, Bamidele da ke sana'ar sayar da katakai ya ce ya tafi makabarta ne ya hako wani gawa kuma ya datse kai da hannun saboda baya samun kasuwa ko kadan wadda hakan ya iyalansa sun gudu sun bar shi.

"Ina hanyar zuwa gidan bokan ne aka kama ni. Ban san gawar wanda na hako ba, na tafi makabarta ne kawai na nemo sassan jikin da na ke bukata," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164