Yadda sakacin gwamnatin APC da Buhari ya jawo asarar sama da ayyuka 12m - Atiku

Yadda sakacin gwamnatin APC da Buhari ya jawo asarar sama da ayyuka 12m - Atiku

- Atiku Abubakar, ya bukaci daukacin al'ummar Nigeria da su sauke Buhari ta hanyar kin zabarsa bisa gazawarsa na cika alkawuran da ya dauk a yakin zaben 2015

- Atiku ya ce a tarihin kasar nan, ba a taba samun mulki mai cike da adalci, walwala, zaman lafiya da bunkasar ilimi kamar a lokacin jam'iyyar PDP ba

- Dan takarar shugaban kasar ya jaddasa cewa, idan har aka bashi dama, zai hada tawagar mutane mafi kwarewa da zasu dawo da martabar tattalin arziki a Nigeria

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci daukacin al'ummar Nigeria da su sauke shugaban kasa mai ci a yanzu Muhanmadu Buhari ta hanyar kin zabarsa bisa gazawarsa na cika alkawuran da ya dauk a yakin zaben 2015.

Ya bayyana hakan a wajen taron gangamin yakin zabensa na shiyya da aka gudanar a babban filin taro na Mapo, da ke Ibadan.

A wajen gangamin yakin zaben, akwai jiga jigan jam'iyyar PDP da suka halarta, irinsu shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinla; tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel; Sanata Ben Bruce, da kuma tsohon ministan wasanni da muhimman ayyuka, Farfesa Taoheed Adedoja, da dai sauransu.

KARANTA WANNAN: Taka leda: Pele ya ce ko kadan Messi bai kama kafarsa a iya kwallon kafa ba

Yadda sakacin gwamnatin APC da Buhari ya jawo asarar sama da ayyuka 12m - Atiku

Yadda sakacin gwamnatin APC da Buhari ya jawo asarar sama da ayyuka 12m - Atiku
Source: Facebook

Atiku ya ce: "A 2015, wasu makaryata, marasa imani suka zo wannan waje don yaudararmu kuma muka basu kuri'unmu. Sai dai mun gano cewa sun kasa cika alkawuran da suka daukarwa al'ummar Nigeria. A tarihin kasar nan, ba a taba samun mulki mai cike da adalci, walwala, zaman lafiya da bunkasar ilimi kamar a lokacin jam'iyyar PDP ba.

" Shi (Buhari) ya yi mana alkawarin samar da ayyukan yi. Amma a maimakon hakan, an rasa sama da guraben ayyuka 12m. Sun yi alkwarin kawar da talauci amma kasarmu ce shelkwatar kasashe masu fama da ukubar talauci. Shin irin wannan gwamnatin ce kuke so taci gaba da mulkarku? Idan har aka bani dama, zamu dawo da martabar wannan kasar tamu.

"Kowa ya san cewa ina jagorantar tawagar kwararru kan tattalin arziki a kasar nan. Idan har aka sake bani sama, zan hada tawakar mutane mafi kwarewa da zasu dawo da martabar tattalin arziki a kasar. Kowa ya san shiyyar Kudu maso Yamma da kaurin suna wajen ilimi, idan aka bani dama, zan tabbata na dawo da martabar ilimi a wannan shiyya."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel