Rundunar sojin Najeriya na bukatar N9bn don siyan takalman sojoji a duk shekara

Rundunar sojin Najeriya na bukatar N9bn don siyan takalman sojoji a duk shekara

- Hukumar bincike da bunkasa tsaro, ta ce rundunar sojin Nigeria na bukatar akalla N9bn don samar da talman da sojojin kasar ke bukata a kowacce shekara

- Darakta janar na hukumar ya ce rundunar sojin Nigeria da suka hada da rundunar sojin kasa, ruwa, da kumana sama, na amfani da kayayyakin da aka sarrafa daga leda a kullum

- AVM Jomo Asahor, ya ce akwai kiyascin kashe N30,000 akan kowanne takalmi mai karko (Bates), sannan N15, 000 akan takalmin yaki, wanda zai ishi jami'an soji 200,000

AVM Jumo Osahor, darakta janar na hukumar bincike da bunkasa tsaro, Abuja ya ce rundunar sojin Nigeria na bukatar akalla N9bn don samar da talman da sojojin kasar ke bukata a kowacce shekara.

Osahor ya bayyana hakan a cikin wata makala daya gabatar a taron shekara shekara karo na 3, wanda kungiyar fasahar sarrafa leda da sinadarai ta Nigeria SLTCN ke shiryawa, a kwalejin kimiyya da fasahar sarrafa leda NILEST, da ke Samaru, Zaria, jihar Kaduna.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ruwaito cewa taron an gudanar da shi karkashin taken: "Gudunmowar kimiya da fasahar sarrafa leda ga tattalin arziki da tsaron kasa."

KARANTA WANNAN: Wata sabuwa: Magu ya karayata masu cewa ya halarci taron nuna goyon baya ga Buhari

Rundunar sojin Najeriya na bukatar N9bn don siyan takalman sojoji a duk shekara

Rundunar sojin Najeriya na bukatar N9bn don siyan takalman sojoji a duk shekara
Source: Facebook

Haka zalika NAN ta ruwaito cewa kwamandan ya yi jawabi kan: "Samar da kayayyakin da aka sarrafa daga leda da kuma kayan jami'an soji: Mahangar rundunar sojin Nigeria."

"Rundunar sojin Nigeria na bukatar akalla N9bn wajen samar da takalma ga kafatanin sojojin kasar a kowacce shekara.

"Wadannan makudan kudaden idan har aka turasu zuwa ga masana'antar sarrafa leda dake Nigeria, zai taimaka matuka wajen farfado da fannin da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar dama fanni tsaro, tare da samar da ayyuka ga matasa.

"Sai dai har yanzu masana'antar sarrafa leda ta Nigeria bata samu damar samun wannan gagarumar garabasar ba daga bukatar kayan da aka sarrafa daga leda a rundunar sojin Nigeria."

Ya ce rundunar sojin Nigeria da suka hada da rundunar sojin kasa, rundunar sojin ruwa, da kuma rundunar sojin sama, na amfani da kayayyakin da aka sarrafa daga leda a matsayin kayayyakin amfaninsu na yau da kulum.

"Akwai kiyascin kashe N30,000 akan kowanne takalmi mai karko (Bates), sannan N15, 000 akan takalmin yaki, wanda za a samawa akalla jami'an soji 200,000," a cewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel