Maigidanci ya lakada ma Uwargidarsa dan banzan duka har lahira saboda rashin jituwa

Maigidanci ya lakada ma Uwargidarsa dan banzan duka har lahira saboda rashin jituwa

Rundunar Yansandan jahar Ogun ta kama wani mutumi, Shina Kasali da laifin kisan kai bayan ya halaka matarsa mai suna Sofiyat a jahar Ogun kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito lamarin ya faru ne a gidan ma’auratan dake unguwar Agabado cikin karamar hukumar Ifo ta jahar Ogun, inda Kasali mai shekaru 38 ya lakada ma Sofiyat dan banzan duka har sai da ta mutu.

KU KARANTA: Kalli yadda ma’aikata suka wulakanta shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki

Yansanda sun bayyana cewa wani makwabcn ma’auratan ne ya bayyana ya kai musu rahoto, inda ya bayyana abinda ya kawo rigimar shine Sofiyat ta dauki baho zata fita diban ruwa, amma mijinta yace bai yarda ta fita ba.

Hana matar fita ne ya janyo kace nace tsakaninsu, inda har ta kai ga an shiga baiwa hammata iska a tsakaninsu, a yayin haka ne Mijin ya samu galaba akan matar ya dinga dukanta har sai da ya kasheta.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Osun ta yi ram da wani Limamin Masallaci da abokansa guda uku da laifin satar wani mutum, Victor Akinbile tare da kasheshi ba tare da wani hakki ba, sai dai kawai don ya kasa biyansu naira miliyan uku kudin fansa.

Kwamishinan Yansandan jahar, Fimihan Adeoye ne ya sanar da haka ne a ranar Talata 4 ga watan Nuwamba inda ya bayyana sunayen mutanen kamar Liman Bashir Owolabi, Rafiu Ahmed, Sunday Kayode da Rasheed Waheed.

A cewar kwamishina Fimihan mutanen sun aikata laifinne a ranar 27 ga watan Nuwamba a gidansa dake cikin karamar hukumar Ifelodun, inda yace sun yi garkuwa da Akinbile ne a ranar Talata 27 ga watan Nuwamba ranar daya baro Legas zuwa Osun don kai ma kakarsa ziyara.

Bayan sun yi garkuwa da Akinbile ne, sai suka tilasta masa ya basu naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa, inda nan take ya tura musu naira miliyan biyar cikin asusun guda daga cikinsu, daga bisani kuma suka kaishi bayan gari, suka sanyashi a cikin sundukin motar, suka banka mata wuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel