Aisha Alhassan ta fara kamfen, ta bukaci matasa da su yi watsi da dabar siyasa

Aisha Alhassan ta fara kamfen, ta bukaci matasa da su yi watsi da dabar siyasa

Tsohuwar ministar harkokin mata, Sanata Aisha Jumai Alhassan ta bukaci matasa da kada su bari yan siyasa su yi amfani da su a matsayin yan dabar siyasa.

Aisha wacce ta kasance yar takara a jam’iyyar United Democratic Party, ta yi wannan rokon ne a Jalingo a ranar Talata, 4 ga watan Disamba lokacin kaddamar da kwamitin kamfen dinta da kuma tanadin da tayi wa jihar Taraba.

Tsohuwar ministar ta shawarci matasa da su nemi sanin tsare-tsare da manufofin yan siyasa akan ci gaban matasa.

Aisha Alhassan ta fara kamfen, ta bukaci matasa da su yi watsi da dabar siyasa

Aisha Alhassan ta fara kamfen, ta bukaci matasa da su yi watsi da dabar siyasa
Source: Twitter

Ta gargadi shugabannin addini da na gargajiya da su guji tsoma baki a siyasa sannan su dauki dukkanin yan takara a matsayin yayansu a lokaci da bayan zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kakakin APC a Imo ya yi murabus

Ta ce ta bar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa UDP ne saboda rashin adalcin da shugabancin jam’iyyar suka yi mata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel