Idan na zarce a kan mulki, zan karasa irin ayyukan da na fara - Buhari

Idan na zarce a kan mulki, zan karasa irin ayyukan da na fara - Buhari

Labari ya zo mana daga Jaridar Vanguard cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawari idan mutanen Najeriya su ka sake zaben sa a wani karon a 2019, za su ga gagarumin canji a fadin kasar nan.

Idan na zarce a kan mulki, zan karasa irin ayyukan da na fara - Buhari

Shugaban kasa Buhari ya nemi a sake ba sa dama a 2019
Source: Depositphotos

Shugaban kasar ya nuna cewa Najeriya za ta canza muddin aka sake ba sa wani daman a zabn 2019. Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga ‘Yan siyasan kasar da su yi yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Buhari ya bayyana wannan ne lokacin da yake jawabi game da sabon tsarin Jam’iyyar APC da manufar su na 2019 mai taken ‘Next Level’. Shugaban kasar yayi wannan kawabi ne a wani katafaren daki da ke fadar Shugaban kasa na Villa.

KU KARANTA: An dage zaman Majalisa saboda wani babban taro na PDP

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa shekaru 4 masu zuwa, su na da matukar tasiri kan tattalin arzikin kasar nan. Buhari yace Gwamnatin sa za ta bunkasa tattalin arziki ta kuma yi wa jama’a aiki idan har ya zarce a kan karagar mulkin kasar.

Buhari yace ya rage na jama’a su zabi a gyara Najeriya ko kuma a koma gidan jiya, inda daidaikun jama’a kurum ke amfana da romon Gwamnati. Buhari yace yayi kokarin ganin ya sauke nauyin da ya dauka cikin shekaru 3 da yayi yana mulki.

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaban sa inda yake neman jama’a su kara ba sa wata damar domin ya karasa irin ayyukan da ya soma. Buhari yace yayi kokarin maganin Boko Haram da samar da ayyuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel