Za mu sake dawowa: Fusatattun 'yan fashi sun aika takarda gidajen jama'ar da su ka gudu

Za mu sake dawowa: Fusatattun 'yan fashi sun aika takarda gidajen jama'ar da su ka gudu

Wasu 'yan fashi masu karfin hali sun tafi sata a wani gida mai dakuna uku da Grace Estate na unguwar Iyesi da ke karamar hukumar Odo/Ota na jihar Ogun.

'Yan fashin sunyi tsamanin za su tarar da masu gidan a ciki amma abin takaici sai ba su tarar da kowa ba, hakan kuma ya bata musu rai sosai. Saboda babu kowa cikin gidan, yan fashin sai da suka fasa rufin gidan da ke makwabtaka kafin suka samu shiga.

Ko da suka shiga suka tarar ba bu kowa a gidan, yan fashin sun tattare talabijin, decoder da sauran kayayaki kawatta daki masu amfani da lantarki.

'Yan fashin sun gaza shiga sauran dakunnan gidan domin kofar tana da matukar karfi. Ganin cewa sun ga za balle kofan dakunan cikin gidan ya sanya 'yan fashin suka rubuta wasika cikin fushi suka ajiye a cikin gidan saboda idan masu gidan sun dawo su samu sakon.

Za mu sake dawowa: Fusatattun 'yan fashi sun aika takarda gidajen jama'ar da su ka gudu

Za mu sake dawowa: Fusatattun 'yan fashi sun aika takarda gidajen jama'ar da su ka gudu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Goyon bayan Buhari: Wata kungiya ta nemi gwamnan Anambra ya yi murabus

A cikin wasikar, yan fashin sun rubuta: " Za mu sake dawowa fa!!! Allah ya bada sa'a." Babu tabbacin ko sakon nasu addu'a ce ko kuma barazana amma bisa dukkan alamu 'yan fashin suna da niyyar dawowa wannan gidan domin su karasa abinda suka fara aikatawa.

Mai gidan, Mr Ogunyombo ya yi hira da The Nation game da lamarin. Ya ce ya yi tafiya tare da iyalansa na wasu kwanaki ne abin ya faru. Ya kuma bayyana irin barnar da suka yi masa a gidan.

"Na lura sunyi kokarin shiga gida na ta kofa amma bai yiwu ba sai suka shiga da rufin gidan makwabta na. Sun sace decorder da na'urar satelite a parlour na.

"Sunyi kokarin shiga sauran dakunnan amma hakan bai yiwu ba. Ina tsamanin suna sauri ne shiyasa suka fusata suka rubuta wasika suka bar min a kan tebur inda suka yi barazanar cewa za su dawo." inji shi.

Tuni an shigar da kara zuwa caji ofis kuma kakakin rundunar yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce nan gaba zai yi cikaken bayani a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel