Hanyoyin da zamu taimakawa Ganduje har Buhari ya samu kuri'u 5m a Kano - Gude

Hanyoyin da zamu taimakawa Ganduje har Buhari ya samu kuri'u 5m a Kano - Gude

- Builder Abdulkadir Yusuf Gude, ya zayyana wasu hanyoyi da kungiyarsa zasu bi wajen taimakawa Ganduje, don ganin cewa Buhari ya samu kuri'u 5m a Kano

- Builder Gude ya bayyana cewa cewa zai tabbatar da cewa gwamnan ya cika wannan alkawari nasa ta hanyar kungiyarsu ta Kanawa for Buhari (KFB)

- A cewarsa, a yanzu haka KFB na da mambobi 500,000 a fadin jihar, kuma suna ci gaba da samun karuwar sabbin mambobi kowacce rana

Wani tsohon mamba da suka kafa jam'iyyar PDP a jihar Kano, kuma wanda ya tsaya takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar, Builder Abdulkadir Yusuf Gude, ya zayyana wasu hanyoyi da kungiyarsa zasu bi wajen taimakawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, don tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri'u 5m a Kano kamar yadda gwamnan yayiwa Buhari alkawari.

Builder Gude, wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau, ya shaidawa jaridar Daily Trust a Abuja cewa kungiyarsa zata tabbatar da cewa gwamnan ya cika wannan alkawari nasa ta hanyar mambobin kungiyarsu ta Kanawa for Buhari (KFB)

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Wanda ya kafa kungiyar Yarabawa ta OPC, Frederick Fasehun ya mutu

Hanyoyin da zamu taimakawa Ganduje har Buhari ya samu kuri'u 5m a Kano - Gude

Hanyoyin da zamu taimakawa Ganduje har Buhari ya samu kuri'u 5m a Kano - Gude
Source: UGC

A cewarsa, a yanzu haka KFB na da mambobi 500,000 a fadin jihar.

"Yawan adadin mambobin zai ci gaba da haurawa a cikin kankani lokaci. Karnin sayen kuri'u ya kare. Kungiyar KFB za ta ci gaba da zagayawa lungu da sako don wayar da kan masu zabe a Kano, da su zabi 'yan takarar da suka aminta da su kuma suke da yakini akansu, kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari," a cewar Builder Gude.

A yayin da yake bukatar 'ya Nigeria da su sanya ci gaban kasar a zukatansu a farkon komai kafin nasu ra'ayin, ya kara da cewa: "Lokaci ya yi da zamu rufe kunnuwanmu da idanuwanmu daga abubuwan da zasu kawo mana rudani kana mu mayar da hankali wajen gina kasar kamar yadda shugaban kasa Buhari ya ke kanyi."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel