Boko Haram: Har yanzu muna fuskantar hare hare - Shehun Borno ya shaidawa Buhari

Boko Haram: Har yanzu muna fuskantar hare hare - Shehun Borno ya shaidawa Buhari

- Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garba Elkanemi, ya karyata ikirarin jami'an tsaro na cewar rundunar soji na samun gagarumar galaba a yaki da Boko Haram

- Ya jaddada cewar har yanzu a Maiduguri, jama'a da manoma basa iya fita wajen garin da nisan kiomita 5 ba tare da 'yan ta'adda sun kashe su ko sun yi garkuwa da su ba

- Shehun Borno, a yayin da yake jinjinawa shugaban kasa Buhari a kokarinsa na yaki da Boko Haram, ya roki gwamnatin tarayya da ta sauya salon yaki da 'yan ta'addan

Mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garba Elkanemi, ya karyata ikirarin jami'an tsaro na cewar rundunar soji na samun gagarumar galaba akan yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno da yankin tabkin Chadi.

Ya jaddada cewar har yanzu a Maiduguri, babban birnin jihar, jama'a da manoma basa iya fita wajen garin da nisan kiomita 5 ba tare da 'yan ta'adda sun kashe su ko sun yi garkuwa da su ba.

Wannan batu na basaraken, ya biyo bayan rokon da kungiyar kwadago ta yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya, na ya gaggauta korar gaba daya shuwagabannin tsaron kasar da masu jagorantar hukumomin tsaro tare da kafa kwamiti mai karfi da zai gaggauta gano musabbabin yadda Boko Haram ta samu damar kashe sama da sojoji 100 a kauyen Metele da ke cikin jihar Borno.

KARANTA WANNAN: 2019: Majalisar wakilan tarayya ta gargadi Kudu maso Gabas akan kauracewa zabe

Boko Haram: Har yanzu muna fuskantar hare hare - Shehun Bornon ya shaidawa Buhari

Boko Haram: Har yanzu muna fuskantar hare hare - Shehun Bornon ya shaidawa Buhari
Source: Twitter

Basaraken ya bayyana hakan a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai masa ziyara a fadarsa gabanin zuwa wajen taron hafsan rundunar sojin kasa, inda ya kasance bako na musamma a taron.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa farmakin da 'yan ta'adda suka kai a wasu kauyuka na Bale Shuwa, Mammanti da sauran garuruwan da ke makwaftaka da Konduga, karamar hukumar Mafa, ya yi sanadin mutuwar sama da manoma 20 da ke girbi a gonakinsu.

Shehun Borno, a yayin da yake jinjinawa shugaban kasa Buhari a kokarinsa na yaki da Boko Haram, ya ce har yanzu akwai muhimman abubuwan da gwamnati ya kamata tayiwa jama'ar jihar don karesu daga hare haren mayakan Boko Haram.

Ya ce: "Hakika abun takaici ne, duk da irin kokarin da gwamnatinka take yi na yaki da 'yan ta'adda don tabbatar da zaman lafiya a garuruwan shiyyar Arewa maso Gabas, har yanzu mu al'ummar jihar Borno muna fuskantar hare hare daga mayakan Boko Haram.

"Babu wanda ya isa ya fita daga Maiduguri da nisan kilomita sama da biyar zuwa goma ba a kauyukan da ke nan hanyar Maiduguri zuwa Damboa zuwa Biu ba tare da mayakan Boko Haram sun far masa ba.

"Muna rokon gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro na kasar da su sake fasalin yadda zasu kawo karshen wannan ta'addanci na mayakan Boko Haram."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel