2019: Dan majalisar wakilai na APC ya sauya sheka zuwa SDP

2019: Dan majalisar wakilai na APC ya sauya sheka zuwa SDP

- Har yanzu guguwar sauya sheka na kadawa a majalisar dokokin kasar

- Sauya shekar yan majalisa yafi shafar jam’iyyar APC mai mulki

- Wani dan majalisa na APC ya sake sauya sheka zuwa SDP

Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta sanar da sauya shekar wani dan majalisar wakilai mai ci daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyarta.

A cewar sanarwa daga babban sakataren labarai na SDP, Malam Mohammed Alfa, dan majalisan da ya sauya shekar shine Honourable Salisu Koko mai wakiltan mazabar Maiyama/koko-Besse, a jihar Kebbi.

2019: Dan majalisar wakilai na APC ya sauya sheka zuwa SDP
2019: Dan majalisar wakilai na APC ya sauya sheka zuwa SDP
Asali: Depositphotos

Alfa ya bayyana cewa cikin kasa da makonni iyu, yan majalisar APC biyu kenan suka sauya sheka zuwa jam’iyyarta.

Kakakin SDP ya kara da cewa suna sanya idanun samun Karin yan majalisar wakilai a yan kwanaki masu zuwa “domin SDP ta kasance jam’iyya mai kula da yi wa mambobinta adalci fiye da sauran jam’iyyu."

KU KARANTA KUMA: Ma su garkuwa da mutane sun sace mataimakin kwanturola na kwastam

A wani lamari makamancin wannan mun ji cewa wani sanata a jam'iyyar PDP, Sanata Joshua Lidani, ya sauya sheka daga jam'iyyarsa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Ahmad Lawan (APC, Yobe) sanar da sauya shekar Lidani a zaman da majalisar na ranar Laraba. Lidani, wanda tsohon gwamnan jihar Gombe ne, na wakiltar mazabar Gombe ta Kudu a majalisar dattijai ta kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel