Hukumar EFCC tayi babban kamu, ta kwace manyan motoci 29

Hukumar EFCC tayi babban kamu, ta kwace manyan motoci 29

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa wato EFCC a ranan Talata, 27 ga watan Nuwamba 2018 ta kwace motoci 29 daga hannun wani dilan motoci, Astrax Auto Shop.

An kai wannan hari ne bisa ga rahoton leken asiri da hukumar ta samu kan ayyukan da masu shagon motocin keyi na damfarar yanar gizo.

Bincike ya nuna cewa dilolin motocin wadanda suka kware wajen damfarar yanar gizo a kasar Amurka sun kasance suna turo kudaden da suka samu daga aikin damfara wani asusun banki.

Hukumar EFCC tayi babban kamu, ta kwace manyan motoci 29
Hukumar EFCC tayi babban kamu, ta kwace manyan motoci 29
Asali: Twitter

Bayan damfaran, sai suyi amfani da kudin wajen odan motoci daga Amurka su turo Najeriya domin sayarwa.

Kafin yanzu, hukumar EFCC ta damke wani mamban yan damfaran, Olusegun Micheal Adeyemi.

Hukumar EFCC tayi babban kamu, ta kwace manyan motoci 29
Hukumar EFCC tayi babban kamu, ta kwace manyan motoci 29
Asali: Instagram

A jawabin da Adeyemi ya baiwa EFCC, ya tabbatar da cewa wani Tayo Onilogbo ne shugaba kuma diraktansu a kamfanin sayar da motocin.

Motocin da aka kwato sune Toyota Corolla hudu; Toyota Camry bakwai; Toyota Highlander biyu; Toyota Venza biyu; Range Rover biyu; Ford SUV daya; Mercedes Benz uku; Toyota 4runner daya; Toyota Sienna daya; Honda Accord hudu; Toyota Sequoia daya da Kia daya.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng