Ba tare da rufe fuska ba: Yan fashi sun sace jarirai 3 a asibitin koyarwa na Calabar

Ba tare da rufe fuska ba: Yan fashi sun sace jarirai 3 a asibitin koyarwa na Calabar

- Rahotanni sun bayya cewa wasu 'yan fashi suka kutsa cikin asibitin koyarwa na jami'ar jihar Calabar, tare da sace wasu jarirai guda ukku

- Yan fashin, wadanda basu sakaya fuskokinsu da wani kyalle ko hula ba, suna dauke da makamai, sun gudanar da aika aikar a cikin kasa da mintuna 10

- Sai dai wani babban darakta na asibitin, Farfesa Thomas Agan, ya karyata faruwar wannan lamari a lokacin da aka tuntube shi a wayar tarho a ranar Litinin

A cikin wani rahoto na kai farmakin ban mamaki a wani asibiti, Legit.ng ta tattara bayanai kan yadda wasu 'yan fashi suka kutsa cikin asibitin koyarwa na jami'ar jihar Calabar, tare da sace wasu jarirai guda ukku.

Haka zalika, daga shafin WuzupNaija, mun kara samun rahoto kan cewa 'yan fashin sun kuma samu nasarar arcewa da wasu kudade.

Rahotanni dai sun bayyana cewa 'yan fashin sun dira a sashen kula da kananan yara na asibitin, inda suka ci zarafin malamar lafiya dake aiki a lokacin, tare da wasu mata masu juna biyu, gami da sace wayoyin hannu dana girkewa.

KARANTA WANNAN: Yajin aiki: An tashi baram baram a zaman sulhu tsakanin Gwamnatin tarayya da ASUU

Ba tare da rufe fuska ba: Yan fashi sun sace jarirai 3 a asibitin koyarwa na Calabar
Ba tare da rufe fuska ba: Yan fashi sun sace jarirai 3 a asibitin koyarwa na Calabar
Asali: Twitter

Yan fashin dai sun gudanar da wannan aika-aikar ne a cikin kasa da mintuna 10.

'Yan fashin, wadanda basu sakaya fuskokinsu da wani kyalle ko hula ba, suna dauke da makamai, wanda ya basu sauki wajen shiga cikin sashen haihuwa, tare da bi gado-gado suna daukar jarirai.

Sai dai wani babban darakta na asibitin, Farfesa Thomas Agan, ya karyata faruwar wannan lamari a lokacin da aka tuntube shi a wayar tarho a ranar Litinin.

Bisa bincike da aka gudanar, an gano cewa tun a watannin baya, jami'an tsaro da suka hada da na 'yan sanda sun janye aiki daga tsaron asibitin, bisa rashin biyan albashi na tsawon watanni.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng