Bidiyon Ganduje: Dukkan mutanen Kano sun zama abubuwan kyama a idanun duniya - Kwankwaso
Rahotanni sun kawo cewa tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya, Dr Rabiu Kwankwaso ya yi tsokaci akan bidiyon Gwamna Ganduje wanda ake zargin shi da karban cin hancin daloli karon .
Kwankwaso ya bayyana cewa ya dade da samun labarin bidiyon tunma kafin a yada shi amma yace kada a yada domin hakan abun kunya ne da kuma zubar da martabar al’umman Kano da addinin Islama.
Sanata Kwankwaso ya ce dukkan mutanen Kano sun zama abubuwan kyama a idanun duniya saboda abin da ake zargin gwamnan jihar da aikatawa.

Asali: Original
Ya ce: "Kafin a fitar da bidiyon na samu labari, amma na ce kar su sake shi. saboda abin kunyar ba kawai na iyalin gwamna ba ne, abu ne da ya shafi martabar mutanen Kano da addininsu da kuma kujerar da na rike mai alheri."
Ya ce gwamna Ganduje masoyinsa ne wanda ya rikida ya koma makiyi.
KU KARANTA KUMA: Yan ta’addan Boko Haram sun kashe manoma 4 a Maiduguri
Sanatan ya kuma ya sha alwashin yin aiki tukuru wajen ganin an sauya gwamnati mai ci wacce ya amta da suna "rubabbiya."
Daga karshe ya jadadda cewa ayyukan da dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Alhaji Abba Kabir ya yi a lokuta daban-daban za su ba shi damar yin nasara a zaben 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng