Najeriya ta maka wasu manyanan kamfanonin mai 2 kotu kan asarar dala biliyan shida

Najeriya ta maka wasu manyanan kamfanonin mai 2 kotu kan asarar dala biliyan shida

Labarin da muka samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa wata kotu a Italiya na tuhumar kamfanin hako mai na Eni da Shell da zargin rashawa a yarjejeniyar cinikin danyen mai wanda har ya kai ga Najeriya yin sarar kudi kimanin dala biliyan shida.

Batun da ke gaban kotun Milan, an bayyana cewa ya shafi tsohon shugaban Najeriya wanda ba a bayyana sunansa ba da kuma wasu tsoffin manyan jami'an kamfanin mai na kasar.

Najeriya ta maka wasu manyanan kamfanonin mai 2 kotu kan asarar dala biliyan shida
Najeriya ta maka wasu manyanan kamfanonin mai 2 kotu kan asarar dala biliyan shida
Asali: UGC

KU KARANTA: An sako tubabbun kwamandojin Boko Haram 155

Legit.ng Hausa ta samu daga BBC Hausa cewa yarjejeniyar ta ba Shell da Eni 'yancin gano wata cibiyar mai a yankin Neja Delta wadda aka kiyasta tana dauke da kimanin biliyan tara na gangar mai.

Ana zargin akwai rashawa a hanyoyin da suka bi wajen samun kwangilar.

An zargi Shell da Eni cewar sun biya gwamnatin Najeriya dala biliyan $1.1 maimakon sun san cewar za a karkatar da kudaden ga cin hanci da rashawa.

Sai dai kamfanonin guda biyu na Italiya da Holland sun musanta zargin, kuma sun shaidawa BBC cewa wannan bacin suna ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng