Malamin Islamiyya ya yi lalata da yar shekara 8 a Kano

Malamin Islamiyya ya yi lalata da yar shekara 8 a Kano

Rahotanni sun kawo cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta damke wani malamin Islamiyya mai shekaru 41, akan zargin lalata wata karamar yarinya mai shekara takwas.

An dai tattaro cewa yarinyar ta kasance daga cikin wasu yara bakwai da aka dauke shi musamman don ya rika koyar da su ilimin addini a gidansu.

Kakakin rundunar yan sandan ta jihar Kano, Sufuritenda Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa sun sami kwararan hujjojin gurfanar da malamin a gaban kuliya, kuma iyayen yarinyar sun yi tsayuwar daka a kan a bi masu hakki.

Malamin Islamiyya ya yi lalata da yar shekara 8 a Kano
Malamin Islamiyya ya yi lalata da yar shekara 8 a Kano
Asali: Depositphotos

Ya ce malamin ya yi amfani da wasu dubaru na janyo hankalin yarinyar har ya yi lalata da ita a bayan gidansu.

A wani lamari makamanccin haka, mun ji cewa wata Kotun Majistire ta bayar da umarnin garkame wasu Mutane biyu a gidan wakafi, Felix Omenihu da Rotimi Amodu, da su ka yi tarayya da juna wajen aikata mummunan laifi na yiwa yarinya 'yar shekara biyar fyade a jihar Legas.

KU KARANTA KUMA: Bamu karbi gudunmawar N10m daga Gwamna Ganduje ba – EFCC

Yayin zartar da umarnin, Kotun ta na zargin wannan Mutane biyu; Omenihu dan shekara 46 da kuma Amodu mai shekaru 39 da laifin aikatawa wannan yarinya mummunan fasadi mai zunubi na kololuwa.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara, Benson Emueri, ya shaidawa kotun cewa ababen zargin biyu sun aikata wannan mummunan laifi a gida mai lamba 3 da ke hanyar Vincent a unguwar Morocco ta jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng