Yanzu-yanzu: Buhari ya kara albashin yan sanda
Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardan Karin albashin ma’aikatan hukumar yan sandan Najeriya a yau Litinin, 26 ga watan Nuwamba, 2018.
A farkon watan nan, Wasika daga hukumar albashi ya nuna cewa an karawa jami’an yan sandan Najeriya albashi. Shugaba hukumar Cif Richard Onwuka Egbule, ya rattaba hannu kan wannan wasika bayan samun umurni daga ofishin hukumar.
Wasikar tace: “Ina mai tabbatar da Karin albashi da canjin tsarin albashin hukumar yan sanda. Wannan kari zai fara aiki ne daga ranan 1 ga watan Nuwamba, 2018 kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar.”
KU KARANTA: Amfanin zogale ga jiki
Yayinda karban bakuncin shugabannin hukumar yan sanda inda suka zo godiya a yau, shugaba Buhari ya bayyana cewa:
“Daga Taraba zuwa Sokoto, zuwa Kudu maso kudu, mutane na cikin tsoro idan basu ga sojoji ba. Ina farin cikin Karin albashi da alawus da sa ran cewa hakan zai kara hazaka da kokarin yan sanda da kuma karfafa tsaron cikin gida.”
“A bar sojoji su dinga manyan ayyuka, ya kamata yan sanda su iya dakile laifuka irinsu fashi da makami, garkuwa da mutane, da sauran su. A kowani kauye, akwai yan sanda a wajen.”

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng