Hotunan hatsabiban 'yan aware na kungiyar IPOB da suka kashe jami'in 'yan sandan Najeriya

Hotunan hatsabiban 'yan aware na kungiyar IPOB da suka kashe jami'in 'yan sandan Najeriya

Rundunar jami'an 'yan sandan Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata sun gurfanar da wasu mutane 'yan kungiyar 'yan aware din nan dake neman tabbatar da kafuwar kasar Biafra watau Indigenous People of Biafra, IPOB, da aka zarga da kashe jami'an su.

Kamar dai yadda muka samu, jami'an 'yan sandan sun bayyana cewa hatsabiban sun kashe masu jami'i ne mai suna Nkwo Nnewi a jihar Anambra a wani kauye da ake cewa Ughelli.

Hotunan hatsabiban 'yan aware na kungiyar IPOB da suka kashe jami'in 'yan sandan Najeriya
Hotunan hatsabiban 'yan aware na kungiyar IPOB da suka kashe jami'in 'yan sandan Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na shiga harkar fim - Garzali Miko

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa a yayin artabun 'yan sandan da dakarun hatsabiban 'yan-awaren, wani Sajant ya rasa ran sa sannan kuma shugaban ofishin shiyyar da wasu mukarraban sa sun jikkata.

A wani labarin kuma, Rundunar sojin Najeriya ta sanar da hannan ta wasu tubabbun manyan mayakan 'yan ta'addan Boko Haram akalla 155 zuwa ga gwamnatocin jahohin Borno, Yobe da kuma Adamawa domin mayar da su cikin iyalan su.

Shugaban shirin rundunar sojin na horarwa tare da sake tsugunnar da 'yan ta'addan Manjo Janar Bamidele Shafa shine ya sanar da hakan lokacin da yake jawabi a wajen bikin mika tubabbun 'yan ta'addan a garin Gombe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng