Ba rabo da gwani ba: Muhimman abubuwa 12 game da marigayi Abba Kyari

Ba rabo da gwani ba: Muhimman abubuwa 12 game da marigayi Abba Kyari

A daren Laahdi 25 ga watan Nuwamba ne Allah ya yi ma tsohon gwamnan yankin Arewa ta tsakiya a zamanin mulkin Soja, Birgediya Abba Kyari rasuwa bayan wata doguwar jinya da yayi, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Legit.com ta ruwaito wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, kuma Da ga mamacin, Mohammed Kyari ne ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa ta shafinsa na Facebook, inda yace babansu ya mutu ne bayan doguwar jinya.

KU KARANTA: Fashola ya kai ziyarar gani da ido zuwa wani muhimmin aiki da Buhari ke yi a Kaduna

Ba rabo da gwani ba: Muhimman abubuwa 12 game da marigayi Abba Kyari
Abba Kyari
Asali: UGC

Don haka muka kawo muku wasu muhimman bayanai game da Kyari, ta yadda masu karatu da basu sanshi ba zasu samu karin haske game da rayuwar mamacin:

- A shekarar 1939 aka haifi Abba Kyari a jahar Neja

- Yayi karatun karamin sakandari a makarantar Borno Middle

- Yayi karatun babbar sakandari a kwalejin Brewa

- Ya shiga aikin Soja a shekarar 1959

- Ya halarci kwas na zama hafsan Soja a 1959 a kwalejin horan Sojoji dake Teshie, Accra, Ghana.

- Ya halarci kwas na zama hafsan Soja a kwalejin Mons Officer Cadet School dake Aldershot a kasar Ingila daga watan Oktoba 1959 zuwa Maris 1960.

- Ya kai mukamin Birgediya Janar a aikin Soja

- Yakubu Gowon ya nada shi gwamnan Arewa ta tsakiya (Kaduna da Katsina) a shekarar 1975

- Shine gwamnan daya fitar da taswirar cikin garin Kaduna

- Ya jagoranci tawagar yan Arewa zuwa taron kundin tsarin mulki na kasa a shekarar 1994

- Ya jagoranci majalisun gudanarwa na kamfanin bankin First Bank, Standard Alliance Insurance da Merchant Bank of Commerce.

- Ya jagoranci kamfanin sarrafa fulawa ta Gamah da kamfanin gine gine ta Alif Engineering and Construction.

Ana sa ran a yau ne iyalansa zasu bada karin bayani game da mutuwar tasa da kuma shirye shiryen yi masa jana’iza, Allah ya jikansa da gafara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng