Shugaba Buharin ya gana da shugabannn tsaro kan harin Matele
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ya jagoranci wata ganaa da shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa Abuja, duk a ckin kokarin ganin an hada dakarun soji da fannin kwararru wajen magance matsalar yan ta’addan Boko Haram.
Da yake tabbatar da lamarin a shafin twitter a Abuja a ranar Lahadi, hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmadm ya ce dukkanin shugabannin tsaro, babban sufeto janar na yan sanda, Idris Ibrahim, da darakta-janar na yan sandan farn kaya (DSS), Yusuf Bichi na daga cikin wadanda suka halarci ganawar.
Shugaba Buhari ya dauki alkawari a ranar Lahadi na tabbatar da cewa za’a toshe duk wata kaa da ya haddasa matsalar.

Asali: Depositphotos
A ranar 18 ga watan Nuwamba ne gamayyar kungiyar Boko Haram na Al Barnawi suka kai hari ga sansanin sojoji Bataliya 157 da ke Matele a yankin arewacin jihar Borno, inda suka kashe sojojin Najeriya da dama.
KU KARANTA KUMA: Za’a iya magance matsalolin Najeriya ta hanyar addu’a – Yakubu Gowon
Sai dai har yanzu hukumomin soji ba su bayar da ainahin adadin mutanen da suka mutu ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng