Dandalin Kannywood: Atiku Abubakar ya sa labule da jaruman 'yan fim din Hausa
Jaruma Fati Mohammed da Jarumi Aminu Shareef Momo sun Jagoranci tawagar Yan masana'antar shirya fina finan Hausa Kannywood zuwa wajen dan takarar Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar don nuna cikakken goyon baya.
A lokacin ziyarar Jaruman sun bayyanawa Alhaji Atiku Abubakar cewar zasu yi amfani da shafukan su da masoyan su wajen mara mishi baya domin cimma gaci.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Dalilin da ya sa na tsunduma harkar fim - Gazali Miko
Legit.ng Hausa ta samu cewa a lokacin ziyarar baya ga Fati Mohammed da Aminu Shareef Momo an ga fuskokin Jarumai da dama ciki harda Balarabe Jaji da Zaharaddeen Sani da Nura Zarge da sauran Manyan Jarumai.
A wani labarin kuma, Tuni dai jarumai irinsu Adam A. Zango da Fati Shu'uma da makamantansu suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Muhammadu Buhari.
Masu sharhi na ganin jaruman Kannywood ka iya sauya akalar zaben 2019, wanda aka kaddamar da yakin neman zabensa ranar Lahadin da ta wuce.
Ga dai bidiyon nan a kasa:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng