Rashin imani: Wani mutum ya kashe budurwa sa yayi balangu da naman ta
Wani labarin rashin imani karara da ya ke cigaba da daga hankulan al'umma shine na wani mutum da ya yanke budurwar sa sannan kuma yayi balangu da naman ta tare da shanye jinin ta duk domin ya kirayi aljani.
Kamar dai yadda muka samu, wannan rashin imanin ya wakana ne a kasar Rasha kuma yanzu haka ma mutumin ya tsufa a gidan yari inda aka kulle shi tsaron shekaru 19 bayan kotu ta tabbatar da aikata laifin nasa.

Asali: Original
Legit.ng ta samu cewa mutumin mai suna Dmitry Luchin kuma mai shekaru 23 a duniya yayiwa budurwar ta sa wadda tsohuwa ce kisan gilla mai suna Olga Budunova, da shekaru 45 ne sannan kuma yayi fata fata da naman ta.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Adamawa sun tabbatar da cafke wani saurayi mai suna Abubakar Yahaya da tsananin kishi ya sa ya guntulewa abokin hamayyara sa mai suna Mohammed Jafar hannu akan budurwa.
Mai magana da yawun rundunar ta 'yan sandan jihar Othman Abubakar shine ya bayyawa manema labarai hakan a hedikwatar su dake a garin Jimeta, Yola
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng