Kiran Allah: Yadda wata baturiya ta rabu da 'ya'yan ta 9 da mijin ta, ta rungumi musulunci

Kiran Allah: Yadda wata baturiya ta rabu da 'ya'yan ta 9 da mijin ta, ta rungumi musulunci

Wata baturiya 'yar kasar Ingila mai suna Heidi Hepworth dake da 'ya'ya akalla 9 ta rabu da su tare da mijin ta kafin daga bisani ta rungumi musulunci ta kuma auri wani dan kasar Gambia dake a Nahiyar Afrika, musulmi.

Matar dai mai shekaru 45 a duniya mun samu cewa ta auri masoyin nata ne dan Afrika mai suna Mamadou Salieu Jallow a watan Nuwambar shekarar da ta gabata.

Kiran Allah: Yadda wata baturiya ta rabu da 'ya'yan ta 9 da mijin ta, ta rungumi musulunci
Kiran Allah: Yadda wata baturiya ta rabu da 'ya'yan ta 9 da mijin ta, ta rungumi musulunci
Asali: UGC

KU KARANTA: Wani matashi ya saki matar sa ya auri uwar ta

Legit.ng Hausa ta samu cewa matar da sabon masoyin nata tuni ma suka kammala shire-shiren yin auren su kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a kasar ta Gambiya.

Wannan lamarin dai yana cigaba da tayar da kura musamman ma a can kasar ta Birtaniya inda mijin nata yake ta ikirarin cewa magance mashi mata akayi amma ba da son ranta ba.

Ita kuwa da take maida martani, matar ta bayyana cewa shigar ta addinin musulunci yanzu ta kara samun natsuwa da kwanciyar hankali ba kamar da ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng