Rikicin makiya da manoma: Buhari ya roki al'ummar Benue da su kara hakuri

Rikicin makiya da manoma: Buhari ya roki al'ummar Benue da su kara hakuri

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki jama'ar jihar Benue da su kara hakuri kan rikicin makiya da manoma da ya salwantar da rayuka da dama a jihar

- Buhari ya yi nuni da cewa wasu mutane ne marasa tsoron Allah a zukatansu ke kashe jama'a a jihohin kasar da sunan makiyaya, ba da sunan addini ko kabilanci ba

- Shugaban kasar ya nuni da cewa tuni jami'an tsaro suka faro gano makwantar 'yan ta'addan kuma suna cafke su

A ranar Juma'a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tawagar masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC na jihar Benue, inda ya bukace su da su taimaka su rokar masa jama'arsu, da su kara yin hakuri dangane da wannan rikici na makiyaya da manoma da ya salwantar da rayuka da dama a jihar.

Da yake jawabi ga tawagar, wacce ta ziyarce shi karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Sanata George Akume, shugaban kasar ya yi nuni da cewa wasu mutane ne marasa tsoron Allah a zukatansu ke kashe jama'a a jihohin kasar da suka hada da Benue, Zamfara da Taraba, amma ba wai rikici na addini ko kabilanci ba.

KARANTA WANNAN: An cafke kanin shugaban kasar Honduran da miyagun kwayoyi a kasar Amurka

Rikicin makiya da manoma: Buhari ya roki al'ummar Benue da su kara hakuri
Rikicin makiya da manoma: Buhari ya roki al'ummar Benue da su kara hakuri
Asali: Twitter

Ya ce: "Kowa dai yasan rayuwar makiyaya. Wadanda aka sani da ke yawo da sanduna, wasu lokutan ka gansu da adduna don sarar ciyawa ga dabbobinsu. Amma a yau wadanda muke gani dauke da bindigogi kirar AK 47, ba zamu kirasu makiyaya ba, kawai dai suna fakewa da sunan su makiyaya ne suna kashe jama'a.

"Muna iya bakin kokarin mu don ganin mun dinke barakar da ake samu a iyakokin kasarmu. Zamu tabbatar an rufe duk wata mashiga ta dabobbi a kasar. Zamu dakile zirga zirgasu. Don Allah ku kara baiwa jama'arku hakuri."

A cewar wata sanarwa daga Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan kafofin sadarwa na zamani da kuma watsa labarai, shugaban kasar ya nuni da cewa tuni jami'an tsaro suka faro gano makwantar 'yan ta'addan kuma suna cafke su.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng