Barayi sun fasa ATM 2 a jami’ar IBB

Barayi sun fasa ATM 2 a jami’ar IBB

Wasu yan fashi sun fasa jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida University (IBBU) dake Lapai, jihar Neja inda suka fasa na’urar ajiyan kudi ta ATM kuma suka debi makudan kudade.

Yan fashin kimanin su 15 sun shiga jami’ar ne sanya da kayan sojoji domin badda kama yadda jami’an tsaron makarantan ba zasu tsaresu ba.

Wani jami’in tsaro wanda ke gadin makarantan ya ce yan fashin sun shiga makarantan misalin karfe 3 na dare cikin motoci uku. Yace sun zo da muggan makamai irinsu bindiga, adduna da sauran su.

Barayi sun fasa ATM 2 a jami’ar IBB
Barayi sun fasa ATM 2 a jami’ar IBB
Asali: Facebook

Yace ana kyautata zaton wani jami’I ne ya sanar da su cewa an zuba kudi cikin na’urar.

KU KARANTA: Hotuna: Ganduje ya raba taransfoma 100 sakamakon rashin wutan lantarki a sassan jihar Kano

Wani jami’in tsaro wanda ya sha duka a hannun su kuma suka harbeshi a kafa yace:

“Ina kula da ginin majalisar makarantan, wanda ke kusa da ATM. Misalin karfe 3 na dare naga wasu mutane sanye da kayan sarki da makamai, sun tsaya a bakin na’urar kuma suka fara kirana.”

“Sun fada min cewa sun kama wasu barayi da suka fasa ATM. Wanna yasa na yarda da su.”

"Sai suka kai ni wani waje inda naga sauran abokan aikina a daure hannu da kafa a kasa."

Dukkanmu muka jikkata kai, hannu, jiki da kafa. Sun yi barazanar kashe duk wanda yayi taurin kai cikinmu.”

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng