Yahoo yahoo: Rundunar 'yan sanda ta cafke wadanda suka kashe dalibar jami'ar Delta
- Rundunar 'yan sanda a jihar Delta ta ce ta samu nasarar cafke mutane ukku bisa zarginsu da kashe wata dalibar jami'ar jihar Delta mai suna Elozino Joshualia Ogege
- Kwamishinan yan sanda na jihar, ya ce an cafke 'yan Yahoo Yahoo guda biyu, sai kuma wani mai gadi, bisa zarginsu da kashe Ogege.
- An tsinci gawar Elozino a wani karamin daji a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2018, bayan da aka sanar da bacewarta a ranar 15 ga watan Nuwamba
Rundunar 'yan sanda a jihar Delta ta ce ta samu nasarar cafke mutane ukku bisa zarginsu da kashe wata dalibar jami'ar jihar Delta mai suna Elozino Joshualia Ogege. Kwamishinan yan sanda na jihar, Mr Muhammad Mustafa ne ya bayyana hakan.
Kwamishinan, ya ce an cafke 'yan Yahoo Yahoo guda biyu, sai kuma wani mai gadi, bisa zarginsu da kashe Ogege.
Elozino, mai shekaru 22, dake shekara ta 3 a bangaren koyon ilimin aikin jarida, an tsinci gawarta ne a wani karamin daji da ke a wajen garin Abraka, jihar Delta, a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2018, bayan da aka sanar da bacewarta a ranar 15 ga watan Nuwamba.
KARANTA WANNAN: Buhari ya sha alwashin karya farashin magunguna a Nigeria

Asali: Depositphotos
Kwamishinan 'yan sandan, ya shaidawa manema labarai a ranar Juma'a a garin Asaba cewa, ana zargin matsafa ne suka kashe dalibar ta jami'ar DELSU.
Ya bata tabbacin kokarin rundunarsa na yin bincike ba sani ba sabo, wajen tabbatar da cewa dukkanin masu hannu a cikin kisan dalibai an cafke su kuma an gurfanar da su don yi masu hukunci.
Mustafa ya ce: "An cafke jigogin da ake zarginsu da aikata kisan, kuma suna kan taimakawa rundunar yan sandan wajen gudanar da bincikenta."
Ya kuma bukaci daukacin jama'a, da su taimakawa rundunar da duk wasu muhimman bayanai da zasu taimaka wajen cafke sauran masu hannu a kashe Miss Elozino Joshualia Ogege.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng