Buhari ya cancanci yin tazarce – Dan majalisar wakilai
Alhaji Bello Dantani, wani dan majalisa mai wakiltan Argungu/Augie a jihar Kebbi a majalisar wakilai ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cancanci tazarce biyo bayan tarin nasarorin da ya samu a mulkinsa.
Dantani ya bayyana hakan a wani hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a birnin Kebbi a ranar Juma’a, 23 ga watan Nuwamba.
Dan majalisan wanda yayi ganawar sirri da Gwamna Atiku Bagudu, yace lamarin tsaro da ya inganta a jihar na daya daga cikin manyan nasarori a gwamnatin Buhari.

Asali: Facebook
A cewarsa gwamnatin APC ta magance matsalar sosai ba da wasa ba ba wai a jihar Kebbi kadai ba harma da jihohin arewacin kasar da dama.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na ganawa da shugabannin APC a Benue
Dantani yayi watsi da zargin jam’iyyun adawa na cewa babu wani ci gaba da aka samu a fannin tsari a fadin kasar.
Dan majalisan yayi kira ga mutanen mazabarsa da su fito kwan su da kwarkwata domin marawa APC baya domin ganin ci gaban kasar a 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng