Wasu iyalai 4 sun kashe yaro dan shekara 9 saboda ya ki yin aikin makaranta

Wasu iyalai 4 sun kashe yaro dan shekara 9 saboda ya ki yin aikin makaranta

Labari da muke samu daga wata majiya ta rundunar 'yan sanda a kasar Faransa, ta ce an kama wasu yan gida daya su hudu da ake zargi da hallaka wani yaro mai shekara tara a duniya saboda bai yi aikin gida wato home work da aka bashi a makaranta ba.

Wannan al’amari dai ya afku ne a birnin Mulhouse da ke gabashin kasar Faransa, shafin BBC Hausa ya ruwaito.

'Yan sanda sun ce, an yi wa yaron mugun duka ne da tsintsiya, inda a wajen kuma akwai babban wansa da yayinsa mata biyu.

Koda ya ke a lokacin da aka daki yaron, mahaifiyarsa ba ta gida amma ta san abinda ke faruwa a gida don haka ne itama aka kamata.

Al'amarin dai ya faru ne a ranar Lahadin da ta wuce.

Wasu iyalai 4 sun kashe yaro dan shekara 9 saboda ya ki yin aikin makaranta
Wasu iyalai 4 sun kashe yaro dan shekara 9 saboda ya ki yin aikin makaranta
Asali: UGC

Za dai a gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika gaban shari'a, inda za a bukaci jin ainihin abinda ya faru.

An dai fi zargin yayan yaron wanda ke da shekara 19 da haihuwa da sanadiyyar mutuwar yaron sakamakon dukan ya yi masa tsintsiya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na ganawa da shugabannin APC a Benue

A cikin wani rahoton binciken musabbabin mutuwar yaron da aka gudanar a asibiti, an gano cewa yaron ya mutu ne saboda bugun zuciya, kuma an ga tsinken tsintsiya a tafin kafar yaron duk ya makale.

Mutuwar yaron ta zo ne adai-dai lokacin da majalaisar wakilan kasar ta Faransa da ke kokarin sanya doka a kan azaftarwar da iyaye ke yi wa 'ya'yansu a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng