Jami'an 'yan sanda sun kama wasu gawurtattun 'yan daudu da luwadi 2 a Kano
Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta cafke wasu ‘yan daudu da kuma ke sana'ar luwadi da suke kiran mutane a waya don yin lalata da su, idan kuma ka ki amincewa sai su ce ai tabbas sun yi lalata da kai sannan sai su yi barazanar sai ka basu kudi.
'Yan luwadin dai kamar yadda muka samu, idan har basu samu yadda suke so ba daga ga mutumin da suka kira, to sukan yi masa barazanar shiga kafafen yada labarai domin su 'tona asirin sa' ko kuma ta kafofin sada zumunta.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Harin Boko Haram: Atiku yayiwa iyalan mamata sha-tara ta arziki
Legit.ng Hausa ta samu cewa 'yan daudun wadanda ba'a bayyana sunan su ba sun yi wa wani Dan kasuwa irin wannan sharri haka zalika ma da aka kama su sun amsa laifin su tare da nuna nadamarsu.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a shiyyar jihar Bauchi dake a Arewa maso gabashin Najeriya sun sanar da kafa dokar hana dukkan wasu tarukan bubukuwa da shagulgula a cikin kokuwar garin saboda tsaro.
Jami'an 'yan sandan dai sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'an hulda da jama'ar su, Kamar Abubakar ya fitar ya kuma rabawa 'yan jarida a jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng