Fashi da makami: Kotu ta yankewa mutane 2 hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Babbar kotu da ke Abeokuta, ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da kotun ta samesu dumu dumu da aikata fashi da makami
- Mai shari'ar, ta ce wadanda ake zargin sun yiwa wani Fasto, Olajide Eliphew fashi, inda suka kwace masa motarsa da kudinta ya kai N1.7m sai kuma kwamfutar hannu guda biyu
- Rundunar 'yan sanda tace wannan laifi ya ci karo da sashe na 6 (b) kuma hukuncinsa na karkashin sashe na 1 (2)(a) na dokar fashi da makami (hukunci na musamman)
A ranar Alhamis, babar kotu da ke Abeokuta, ta yankewa wasu mutane biyu, Agbarojo Abolore, 39, da Adeniyi Dada, 32, hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da kotun ta samesu dumu dumu da aikata fashi da makami.
Mai shari'a Olatokunbo Majekodumi, wacce ta yanke wannan hukunci ga Abolore da Dada, ta ce mai shigar da karar ya gabatar da hujjojin da suka tabbatar da zargin da ake yiwa mutanen biyu na hadin kai da yin fashi da makami.
"Bayan da kotu ta sami wadanda ake zargi da aikata laifukan da ake tuhumarsu da shi, kotu ta yanke maku hukuncin kisa ta hanyar rataya, Allah ya yi rahama a gareku," a cewar Majekodunmi.
KARANTA WANNAN: Dogaro da kai: Ganduje ya dauki nauyin horas da mata 100 sana'ar kanikancin mota

Asali: Twitter
Da take bitar shari'ar, ta ce wadanda ake zargin sun yiwa wani Fasto, Olajide Eliphew fashi, inda suka kwace masa motarsa kirar Nissan Pathfinder Jeep 2003, kalar toka, da kudinta ya kai N1.7m sai kuma na'urorin kwamfutar hannu guda biyu da kudinsu ya kai N180,000.
"Wadanda ake zargin da tawagarsa sun farwa Fasto Olajide jim kadan bayan da ya tashi daga aikinsa na dare inda suka tsareshi da bindigogi tare da yi masa barazanar ko dai ya basu makullin motarsa ko su kashe shi," a cewar ta.
Rundunar 'yan sanda tace wannan laifi ya ci karo da sashe na 6 (b) kuma hukuncinsa na karkashin sashe na 1 (2)(a) na dokar fashi da makami (hukunci na musamman), karkashin dokar Rll ta gwamnatin Nigeria, 2004.
Rundunar ta ce wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2012 a gida mai lamba 1, titin Olajide Eliphew, Papa Ibafo a jihar Ogun.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng