Dogaro da kai: Ganduje ya dauki nauyin horas da mata 100 sana'ar kanikancin mota

Dogaro da kai: Ganduje ya dauki nauyin horas da mata 100 sana'ar kanikancin mota

- Gwamnatin jihar Kano za ta dauki nauyin horas da mata 100 sana'ar kanikancin mota karkashin shirin hadin guiwarta da kamfanin Peugeot na Nigeria (PAN)

- Kwmaishiniyar harkokin mata ta jihar, Hajiya Yar'dada ta ce a baya baya, gwamnatin jihar Kano ta horas da mata 50 kan kanikan mota a kamfanin na PAN

- A nashi jawabin, shugaban Digital Bridge Institute, Injiniya Titi Omo-Ettu yace a zangon karatun makarantar na 2018/2019, dalibai 104 ne aka yaye

Gwamnatin jihar Kano za ta dauki nauyin horas da mata 100 sana'ar kanikancin mota karkashin shirin hadin guiwarta da kamfanin sarrafa motocin Peugeot na Nigeria (PAN), a jihar Kaduna.

Kwmaishiniyar harkokin mata ta jihar, Hajiya Yar'dada Maikano Bichi ta bayyana hakan a wani taron yaye dalibai karo na biyu na wata makaranar koyar da sana'o'i kan sanarwar na'urori mai suna 'Digital Bridge Institute’s National Innovation' da ke koyar da dalibai har zuwa matakin Diploma

Hajiya Yar'dada ta ce a baya baya, gwamnatin jihar Kano ta horas da mata 50 kan kanikan mota a kamfanin na PAN.

KARANTA WANNAN: 2019: Ba zaka yaudari Kudu maso Gabas da alkawuran karya ba - PDP ta gargadi Buhari

Dogaro da kai: Ganduje ya dauki nauyin horas da mata 100 sana'ar kanikancin mota
Dogaro da kai: Ganduje ya dauki nauyin horas da mata 100 sana'ar kanikancin mota
Asali: Depositphotos

"Gwamnatin jihar Kano ta dukufa wajen ganin cewa ta bunkasa rayuwar mata. A bayyana yake cewa gwamnatin jihar ta yi abubuwa da yawa da suka taba rayukan matan jihar. Gwamnatin jihar karkashin Ganduje ta dukufa wajen ganin cewa suma mata an dama da su," a cewarta.

A nashi jawabin, shugaban hukumar gudanar na makarantar ta Digital Bridge Institute, Injiniya Titi Omo-Ettu yace a zangon karatun makarantar na 2018/2019, dalibai 104 ne aka yaye, wanda kuma babban burin makarantar shine baiwa dalibai horo na musamman kan sana'o'in dogaro da kai da zai basu damar samun matsagunni a fannin harkokin sadarwar na'u'rori.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng