Majalisar dokokin jihar Sokoto ta tabbatar da Dan'Iya a matsayin mataimakin gwamnan jihar

Majalisar dokokin jihar Sokoto ta tabbatar da Dan'Iya a matsayin mataimakin gwamnan jihar

A yau Alhamis, 22 ga watan Nuwamba, 2018 ne Majalisar dokokin jihar Sokoto ta tabbatar da Alhaji Mannir DanIya a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Mun kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya aika sunan Manni DanIya majalisar domin tabbatar da shi a matsayin mataimakinsa bayan tsohon mataimakinsa yayi murabus.

A ranan 13 ga watan Nuwamba, mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Aliyu, ya yi murabus daga kujeransa bayan ya samu tikitin takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress APC.

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta ta tabbatar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, a matsayin dan takaran gwamnan jihar na zaben bana karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Game da cewar jaridar New Telegraph, kwamishanan hukumar INEC kan ilimantar da msu zabe, Festus Okoye, ne ya tabbatar da hakan.

A kwanakin baya da hukumar ta saki jerin sunayen yan takara, an nemi sunan gwamna Aminu Waziri Tambuwal an rasa.

Okoye yace: “Jam’iyyar PDP tayi amfani da lokacin da hukumar ta bada na daman iya sauya sunan dan takara wajen sanya sunan Tambuwal.”

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng