Boko Haram: Najeriya za ta fara kai harin jiragen yaki daga Jamhuriyar Nijar

Boko Haram: Najeriya za ta fara kai harin jiragen yaki daga Jamhuriyar Nijar

Babban hafsan Sojojin Sama, Abubakar Sadique, ya bayyana cewa jami’an sojin sama za su girka sansanin makamai a Difa da ke cikin Jamhuriyar Nijar, domin kai wa yan ta’addan Boko Haram farmaki.

Abubakar ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke jawabin rufe taron masana na duniya a kan harkokin tsaron kasa ta sararin samaniya a babbar birnin tarayya, Abuja, a ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba.

A cewarsa wannan sansani da za a kafa zai dauki wani sabon salo wajen samun nasarar kakkabe hare-haren yan ta’addan a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Ya kuma bayar da albishir cewa akwai karin hadin kai da goyon bayan da ke tafe daga wasu kasashe na Turai, Gabas Ta Tsakiya, Asiya da Amurka da ma Afrika.

Boko Haram: Najeriya za ta fara kai harin jiragen yaki daga Jamhuriyar Nijar
Boko Haram: Najeriya za ta fara kai harin jiragen yaki daga Jamhuriyar Nijar
Asali: Twitter

Ya ce shiri ne da za'a yi wa matsalar Boko Haram taron-dangi domin yin maganinta na din-din-din, saboda yaki da ta’addanci abu ne da ya buwayi duniya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: EFCC ta rufe kadarar Fayose da ke Ado-Ekiti

Ya kuma shaida wa manema labarai cewa babu kasar da za ta iya yaki da ta’addanci ita kadai. Ya ce sai an hada da taimako da goyon bayan jama’ar da ke da irin wannan matsalar kuma suka fahimci irin barazanar da ta’addanci ke da shi nan gaba a gare su.

Ya ce daga yanzu jiragen yaki za su rika tashi daga Difa cikin Jamhuriyar Nijar su kai hare-hare kan Boko Haram su koma. Maimakon a ce sai sun tashi daga Maiduguri sun kai hari, kuma su sake komawa Maiduguri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng