Dangote ya ginawa ABU Zaria katafaren dakin kwanan dalibai na zunzurutun kudi har N1bn
- Gidauniyar tallafi ta Dangote ADF ta ce ta kammala shirye shirye na kaddamar da katafaren dakin kwanan dalibai da ta gina da zunzurutun kudi har N1bn a jami'ar ABU
- Hukumar makarantar ta ce daga cikin dalibai 50,000 da ke samun gurbin karatu a jami'ar a kowacce shekara, dalibai 13,000 ne kacal ke iya samun dakunan kwana
- Babban manaja kuma CEO na gidauniyar tallafi ta Aliko Dangote, Zouera Youssoufou ta ce tallafawa ilimi na daya daga cikin kudurorin gidauniyar
A wani babban yunkuri, gidauniyar tallafi ta Dangote ADF ta ce ta kammala shirye shirye na kaddamar da katafaren dakin kwanan dalibai da ta gina da zunzurutun kudi har N1bn a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria, jihar Kaduna.
Hukukomin jami'ar, wacce ake kallo a matsayin babbar jami'a a nahiyar Afrika ta Yamma, sun bayyana wannan aikin ginin katafaren dakin kwanan daliban da gidauniyar Dangote ta kammala, a matsayin "samun sauki", wanda ake sa ran zai kawo karshen matsalolin rashin matsugunni da ya dade yana ciwa jami'ar tuwo a kwarya.
Daraktan sashen tsare tsare da ayyukan cikin jami'ar, Injiniya Muhammad Aminu Sambo, ya ce, "Wannan babban sauki ne da jami'ar ta samu kasancewar tana fama da karancin dakunan kwanan dalibai, idan aka kwatanta da yawan daliban da ke samun gurbin karatu a kowacce shekara. Wannan wani mafarki ne da ya zama gaskiya."
KARANTA WANNAN: Rikicin makiyaya da manoma ya yi silar mutuwar mutane da dama a Katsina

Asali: UGC
Da ya ke zantawa da manema labarai, Sambo ya ce daga cikin dalibai 50,000 da ke samun gurbin karatu a jami'ar a kowacce shekara, dalibai 13,000 ne kacal ke iya samun dakunan kwana a cikin jami'ar. Ya jinjinawa shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, tare da bukatar sauran 'yan Nigeria da su yi koyi da hakan a fannin ilimi.
A nashi bangaren, babban mai zane zane na jami'ar ta ABU, Yabani Abubakar, ya bayyana wannan katafaren dakin kwanan daliban a matsayin babban ci gaba, yana mai cewa, ginin ya kunshe bangarori 10, inda akwai dakunan kwana 36 a kowanne bangare.
Abubakar ya ce, za a kaddamar da wannan sabon katafaren dakin kwanan dalibai a bukin yaye daliban jami'ar mai zuwa, a cewarsa, Dangote ya ziyarci dakin kwanan daliban a kwanakin baya, kuma ya bayar da umurnin a kafa sabbin na'u'rorin zamani a ciki kamar fitilu masu amfani da hasken rana.
Babban manaja kuma CEO na gidauniyar tallafi ta Aliko Dangote, Zouera Youssoufou ta ce tallafawa ilimi na daya daga cikin kudurorin gidauniyar, tana mai cewa a baya bayan nan gidauniyar ta bada tallafin $1.25bn ga fannin ilimi.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng