Ba zamu yarda wasu yan tsiraru su sanya hijabi ba - Iyayen dalibai Kirista sun gudanar da zanga-zanga a makaranatar Ibadan

Ba zamu yarda wasu yan tsiraru su sanya hijabi ba - Iyayen dalibai Kirista sun gudanar da zanga-zanga a makaranatar Ibadan

Rikicin hijabin makarantan sakandaren jami’ar Ibadan ya dau sabon salo a jiya Laraba yayinda wasu iyayen dalibai Kirista, marasa addini da wasu iyayen Musulmai suka shiga ofishin mataimakin shugaban makarantan, Farfesa Adeyinka Aderinto, domin bayyana ra’ayinsu kan al’amarin hijabi.

Sun nuna bacin ransu da kungiyar iyaye dalibai Musulmai wadanda sukace wajibi ne a baiwa kowa zabin abinda zai sanya.

Wannan gwagwarmaya da iyayen dalibai Musulman suka fara ya sabbaba kulle makarantan ranan Litinin. An gudanar da ganawan gamayyar malamai da iyaye domin shawon kan al’amarin amma ba’a cimma mafita ba a karshen zaman.

A jiya Laraba, wasu iyayen daliban Kirista suka gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin yardansu da a yadda Musulmai suka taso da maganan Hijabi.

Daga cikin abubuwan da suka fada shine: “Bamu yarda da nuna banbancin addini ba, muna son zaman lafiya a makarantan ISI, Kada ku raba kan yayanmu, bamu son rikicin addini, kada wanda ya canza masa kayan makaranta.”

Mun kawo muku rahoton cewa an kulle makarantan ne bayan rikicin ya faru a inda shugabannin suka hana dalibai mata Musulmai sanya hijabi a makaranta. Dalibai sun dawo makaranta a yau Litinin kamar yadda aka saba sai wata daliba ta shigo sanye da hijabi kuma aka hanata shiga makaranta.

Wannan abu ya fusata iyaye da dalibai jami'ar Ibadan inda suka fito kwansu da kwarkwatansu suka gudanar da zanga-zanga kan wannan rashin adalci.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng